Mutum 2 da Za Su Gabatar da Shaida a Shari'ar Ganduje Sun Fara Fuskantar Hadari a Kano

Mutum 2 da Za Su Gabatar da Shaida a Shari'ar Ganduje Sun Fara Fuskantar Hadari a Kano

  • Shaidun da gwamnatin Kano ke shirin gabatar da su a kotu kan shari'ar tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje, sun fara funkantar barazana
  • Mutanen biyu sun bayyana zaman dar-dar da suke yi tun bayan bayyana aniyarsu ta yin shaida a kotu kan zargin almundanar Ganduje
  • Gwamnatin Kano ta gurfanar da Ganduje da wasu mutane a gaban kotu kan zargin mallakawa kansu hannun jarinta a tashar ruwa ta Dala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa mutum biyu da za su ba da shaida a shari'ar tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, sun fara fuskantar bazarana.

Shaidun dai suna daga cikin wadanda ake ganin suna da matukar muhimmanci a shari'ar da gwamnatin Kano ke zargin Ganduje da karkatar da hakkinta a tashar jiragen ruwa mai darajar biliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Kotu ta ba da umarnin wucin gadi a shari'ar gwamnati da likitoci

Tsohon shugaban APC, Ganduje.
Tsohon shugaban APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje CFR
Source: Facebook

Premium Times ta ce shaidun, Bashir Uba da Ahmad Rabiu, za su ba da bayani a gaban Babbar Kotun Jihar kan shafi'ar dambarwar mallakar kamfanin Dala Inland Dry Port Limited.

Masu gabatar da kara sun shirya shaidu da dama, ciki har da jami’an gwamnati da ake zargin an tilasta su sanya hannu a wasu takardun da suka bada damar kwace hannun jarin gwamnatin Kano.

Halin da shaidun gwamnatin Kano ke ciki

Wani babban shaida, Bashir Uba, tsohon darakta a ma’aikatar kasuwanci ta jihar, ya bayyana cewa ya fahimci rayuwarsa na cikin hadari.

Ya tabbatar da cewa wasu mutane da bai sani ba sun ziyarce shi a gidansa, suka yi masa gargaɗi kan ya janye daga shari’ar.

“A ranar Asabar, ina zaune na ji wasu na buga kofar gidana, saboda tsoro, ban buɗe ƙofar da wuri ba sai da na duba ta wani rami a kofar, na ga wasu mutane biyu da ban sani ba a tsaye."

Kara karanta wannan

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotu game da shugabancin jam'iyyar a Kano

Yadda aka tsorata shaidun gwamnatin Kano

Ya ce mutanen sun bayyana sunansa, sun ambaci lambar wayarsa, har ma da wuraren aikinsa na baya da na yanzu.

“Sun ce kawai sun zo ne don ‘su ba ni shawara.’ Sun gaya mini, ya kamata na nisanta da wannan shari’ar da zan bada shaida. Lokacin da na tambayi wacce shari’a suke nufi, sai suka ce, ‘ka fi mu sani.’”

Bashir Uba ya ce ya riga ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda da lauyansa domin daukar matakin da ya dace

Haka kuma, Ahmad Rabiu, wani shaidar farko a shari'ar Ganduje, ya bayyana yama shakkun wasu abubuwa da ya ga suna faruwa a gida da ofishinsa.

Ganduje da Abba.
Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje da Gwamna Kabir Yusuf na Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Sanusi Bure D-Tofa
Source: Facebook

Dalilin gurfanar da Ganduje a kotun Kano

Gwamnatin Kano ta zargi Ganduje da sauran wanda ake tuhuma da mallakawa kansu 80% na hannun jarin na kamfanin Dala Inland Dry Port, ciki har da 20% na hannun jarin gwamnati.

Masu gabatar da kara sun kuma zargi Ganduje da wasu da karkatar da fiye da ₦4.49 biliyan na kudaden jihar Kano da aka ware domin aiwatar da ayyukan gine-gine, in ji Punch.

Kara karanta wannan

Boye boye ya kare, majalisar Kano ta yi magana kan shirin Gwamna Abba na komawa APC

An samu tsaiko a shari'ar Ganduje

A wani labarin, kun ji cewa an samu tsaiko a zaman sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan Kano , Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da wasu mutum bakwai a babbar kotu.

Gwamnatin Jihar Kano na tuhumar mutane takwas da aikata laifuffuka 11 da suka haɗa da cin hanci, haɗin baki, karkatar da dukiyar jama’a.

Sai dai a wani zaman da kotu ta yi, wadanda ake tuhuma ta hannun lauyoyinsu, sun gaza tura takardun da suka wajaba a kansu kafin fara shari'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262