Shugaban EFCC Ya Fitar da Sababbin Bayanai kan Binciken a Ake Yi Wa Malami

Shugaban EFCC Ya Fitar da Sababbin Bayanai kan Binciken a Ake Yi Wa Malami

  • Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya tabo batun binciken da ake yi wa Abubakar Malami
  • Ola Olukoyede ya bayyana cewa bai da wata matsala da tsohon Ministan shari'ar, kuma ba shi ba ne ya fara bincikarsa
  • Ya kare kansa daga zargin cewa yana yin ramuwar gayya ne saboda wani abin da Malami ya yi lokacin da yake Ministan shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan binciken da ake yi wa Abubakar Malami.

Ola Olukoyede ya ce ba shi da wata matsala ta kashin kai da tsohon Ministan na shari’a kuma tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya.

Shugaban EFCC ya yi bayani kan binciken Malami
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede da Abubakar Malami Hoto: @OfficialEFCC, @aaMalamiSAN
Source: Twitter

Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Janairun 2026 yayin wata tattaunawa a shirin Politics Today na tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An bude sabon bincike bayan gano bindigogi da alburusai a gidan Malami

EFCC ta gurfanar da Abubakar Malami gaban kotu

A watan Disamban 2025, EFCC ta gurfanar da Malami a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin aikata laifuffuka da suka shafi almundahanar kuɗaɗe.

An gurfanar da shi tare da ɗansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da matarsa Bashir Asabe, bisa tuhume-tuhume guda 16.

Malami dai ya zargi cewa tsare shi, bincike a kansa da kuma barazanar gurfanar da shi a kotu dalilai ne na siyasa, musamman bayan da ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC.

Tsohon Ministan shari’ar ya kuma bukaci Olukoyede da ya janye hannunsa daga binciken, yana mai nuni da zargin cewa kwamitin bincike na shari’a da mai shari’a Ayo Salami ya jagoranta ya taba sabon shugaban na EFCC da laifi.

Me shugaban EFCC ya ce kan binciken Malami?

Da yake mayar da martani kan zargin cewa EFCC na nuna wariya ne wajen binciken Malami, Olukoyede ya ce binciken ba na kashin kai ba ne kuma ba na siyasa ba ne.

Kara karanta wannan

Ribas: Gwamna Fubara na tsaka kai wuya, azumi da addu'a kadai za su cece shi

Ola Olukoyede ya jaddada cewa ya gaji takardun binciken ne tun kafin ya zama shugaban hukumar EFCC.

“Har yanzu ban ga hujjar da zai kawo don tabbatar da wannan zargi ba. Ban fahimta ba. Mu a EFCC muna gudanar da bincike ne cikin kwarewa da bin ka’ida."
“Babu wata matsala ta kashin kai a cikin wannan batu. Idan har Najeriya za ta ci gaba, dole ne mu yarda cewa wannan yaki da cin hanci dole ne a yi shi ba tare da nuna bangaranci ba."
“Kuma wannan ne abin da nake so ’yan Najeriya su fahimta su kuma yarda da mu. Binciken wannan mutumin ya fara ne tun kafin na hau wannan mukami. Da yawa ba su san haka ba. Eh, na gaji fayil ɗin binciken ne kawai."

- Ola Olukoyede

An dade ana bincikar Malami

Ya bayyana cewa an shafe kusan shekara biyu da rabi ana gudanar da binciken kafin a yanke shawarar gurfanar da wadanda ake zargi, bayan jami’an bincike sun gamsu cewa hujjojin da aka samu sun cika ka’ida.

Kara karanta wannan

Bayan janye korafi a ICPC, Dangote ya kai karar tsohon shugaban NMDPRA a EFCC

“Abin da na yi kawai shi ne tabbatar da cewa an gudanar da binciken cikin tsanaki da kwarewa. An shafe kusan shekaru biyu da rabi ana binciken wannan shari’a. Fayil ɗin tun kafin na hau ofis aka buɗe shi, kuma na gaje shi ne."
“A cikin shekaru biyu da na shafe a ofis, muna ci gaba da bincike sosai, muna kokarin tabbatar da laifuffukan da ake zargi. Ban yanke shawarar gurfanarwa ba sai bayan da na tabbatar da cewa akwai hujjoji."
“Don haka babu wata maganar tsangwama ko ramuwar gayya. Babu komai na kashin kai a ciki."

- Ola Olukoyede

Shugaban EFCC ya kare kansa kan zargin da Malami ya yi
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Shugaban hukumar EFCC ya kare kansa

Shugaban na EFCC ya kuma yi magana kan zargin Malami na cewa yana daukar fansa ne saboda wai tsohon Ministan yana da hannu wajen kafa kwamitin bincike na mai shari’a Ayo Salami, wanda ake zargin ya taba tuhumar Olukoyede.

“Bari na rufe wannan batu gaba ɗaya. Duk wanda ke cewa an tuhume ni da laifi ko cin hanci ta hanyar rahoton wannan kwamiti, to wajibi ne su fito da rahoton a fili domin jama’a su gani."

Shugaban na EFCC ya jaddada cewa an kafa kwamitin ne a 2020, ya kuma kammala aikinsa a farkon 2021, yayin da Malami ya ci gaba da zama Ministan shari’a har zuwa 2023.

Kara karanta wannan

NLC ta yi wa Tinubu barazana saboda a dakatar da dokokin haraji

An bude sabon bincike kan Malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta fara bincike kan tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami.

Hukumar DSS ta fara bincike kan Malami ne bayan gano wasu bindigogi a gidansada ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Ba a dai bayyana adadin makamai da harsasan da aka gano ba, amma an nuna cewa adadinsu ya kai girman da zai jawo cikakken bincike daga DSS.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng