An Shawo kan Matasan da Suka Farmaki Hausawa da Gidan Sarki a Edo
- Rikicin da ya biyo bayan zanga-zanga kan rashin tsaro a Ekpoma ya lafa bayan ’yan sanda sun ɗauki matakan gaggawa tare da cafke wasu mutane
- An samu firgici a kasuwar dabbobi bayan wasu matasa sun kori Hausawa tare da lalata dukiyoyi, lamarin da ya jawo tsoro da fargaba a garin
- Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike, tare da ƙarfafa tsaro domin hana maimaituwar irin wannan lamari a yankin Ekpoma da kewaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo – Zaman lafiya ya fara dawowa a garin Ekpoma da ke karamar hukumar Esan Ta Yamma bayan ’yan sanda sun shawo kan tarzomar da ta biyo bayan zanga-zanga kan matsalar tsaro a yankin.
Lamarin ya faru ne bayan wata zanga-zanga da aka shirya domin nuna damuwa kan kisan wani matashi da kuma yawaitar sace-sace da garkuwa da mutane a yankin.

Source: Facebook
Kakakin 'yan sandan Najeriya, Benjamin Hundeyin ya wallafa a Facebook cewa zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, inda wasu matasa suka karkatar da ita kan Hausawa.
Yadda aka farmaki Hausawa a jihar Edo
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Asabar, mazauna Ekpoma sun toshe babbar hanya domin nuna fushinsu kan tabarbarewar tsaro, musamman bayan mutuwar wani matashi a daren Juma’a.
A yayin da zanga-zangar ke gudana, wasu fusatattun matasa sun kutsa cikin lamarin, inda suka fara korar ’yan kasuwa Hausawa a kasuwar dabbobi, tare da yanka awaki da lalata kayayyaki.
Wannan ya jefa jama’a cikin firgici, inda aka ga mutane na gudu domin tsira, yayin da wasu dabbobi ke yawo a kan manyan tituna ba tare da kulawa ba.
Matakan da ’yan sanda suka dauka
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya ɗauki matakan gaggawa tun bayan samun bayanan yiwuwar tayar da tarzomar.
Rahoton Punch ya nuna cewa ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki da suka haɗa da shugabannin al’umma da wakilan dalibai domin tattauna hanyoyin kauce wa rikici.
A ranar 10, Janairu, 2026, lokacin da zanga-zangar ta fara, kwamandan yankin Ekpoma ya gaggauta tura jami’ai tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da doka da oda.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya yi Allah-wadai da abin da ya faru, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa gwamnati na aiki tukuru domin hana ramuwar gayya da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Edo: An farmaki gidan Sarkin Ekpoma
Bayan kai farmaki kan Hausawa a kasuwa, rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun kai hari gidan Sarkin Ekpoma, Zaiki Anthony Ehizojie Abumere II.

Source: Facebook
A wani sako da gwamnatin Edo ta wallafa a shafinta na Facebook, gwamna Monday Okpebholo ya ziyarci wajen da abin ya faru tare da gargadi da cewa ba zai lamunci haka ba.
An kashe Hausawa a jihar Edo
A wani labarin, mun kawo muku cewa kwanaki an kashe matafiya 16 ’yan Arewacin Najeriya a jihar Edo bayan an yi musu tuhuma marar hujja.
Wasu ’yan sa-kai sun alakanta su da garkuwa da mutane, lamarin da ya kai ga hallaka su ba tare da gudanar da bincike na gaskiya ba.
Daga bisani, rahotanni sun nuna cewa rundunar ’yan sanda ta cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a wannan mummunan lamari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

