Wata Sabuwa: An Bude Sabon Bincike bayan Gano Bindigogi da Alburusai a Gidan Malami

Wata Sabuwa: An Bude Sabon Bincike bayan Gano Bindigogi da Alburusai a Gidan Malami

  • An sake bude sabon bincike kan tsohon M inistan shari'a, abubakar Malami bayan samamen da hukumar EFCC ta kai gidansa a jihar Kebbi
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa jami'an EFCC sun gano bindigu da alburusi a gidan malami da ke cikin birnin Kebbi
  • Rahoto ya nuna cewa har yanzu Malami bai cika sharuddan belin da babbar kotun tarayya ta ba shi ba, yana tsare a gidan yarin Kuje da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta fara binciken Tsohon Antoni Janar kuma Tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) kan wasu makamai da aka gano a gidansa.

An ruwaito cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ci karo da bindigu da alburusai lokacin da ta kai samame gidan Malami da ke birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya fitar da sababbin bayanai kan binciken da ake yi wa Malami

Abubakar Malami.
Tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) tare da jami'an hukumar gyaran hali Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

An gano makamai a gidan Abubakar Malami

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa hukumar ta mika makaman ga Hukumar DSS don gudanar da cikakken bincike, domin ba ƙarƙashin hurumin EFCC ba ne.

Ba a bayyana adadin makamai da harsasan da aka gano ba a halin yanzu, amma rahotanni sun nuna cewa adadinsu ya kai kololuwa da zai jawo cikakken bincike daga DSS.

Malami, wanda aka ba da belinsa a makon da ya gabata tare da dansa Abdulaziz, da matarsa, har yanzu yana tsare a Gidan Gyaran Hali na Kuje, saboda bai cika sharuddan belin ba.

Malami na neman kaucewa jami'an DSS

Amma wasu majiyoyi sun ce yana ɗaukan matakai a hankali domin jinkirta binciken DSS kan makaman da aka samu a gidansa.

“An fara binciken tsohon ministan kan yadda aka ga makamai a gidansa na Birnin Kebbi. Tuni dai aka mika jerin abubuwan da aka gano ga hukumar DSS.

Kara karanta wannan

Bayan janye korafi a ICPC, Dangote ya kai karar tsohon shugaban NMDPRA a EFCC

"Yanzu ya rage ga Malami ya bayyana wa DSS yadda ya samu makaman, wanda shi ya sa bai cika sharuddan belinsa ba. Yana cikin gidan yari ne domin kaucewa yiwuwar kama shi da DSS ka iya yi.
"Jami’an DSS sun je har cikin kurkukun Kuje domin gayyatar Malami, amma ya samu labarin zuwansu, ya tayar da hankali. Amma dai dole doka zata yi aiki.”

Wata majiya daga cikin hukumar EFCC ta tabbatar da cewa har yanzu Malami bai cika sharuddan belinsa ba, in ji rahoton Punch.

Jami'an hukumar DSS.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya (DDS) a bakin aiki Hoto: @DSSNigeria
Source: Facebook

Yaushe aka fara binciken Malami?

Majiyar ta kara da cewa an fara binciken ayyukan Malami ne tun a lokacin da tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu, yake ofis.

“An ci gaba da binciken har lokacin shugaban rikon kwarya, Ibrahim Chukkol, zuwa shugaban EFCC na yanzu Olukoyede.
"Babu wani abu na hassada a binciken da EFCC ke yi wa Malami tun 2019. Malami ya san wannan lamari," in ji majiyar.

Kotu ta ba da belin Abubakar Malami

A wani rahoton, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami.

Kara karanta wannan

Duk da janye korafin Dangote, ICPC ta taso tsohon shugaban NMDPR a gaba

Mai shari'a Bello Kawu ne ya amince da buƙatar belin a ranar Talata, biyo bayan wani koke da lauyoyin Malami suka shigar gabansa.

A cewar kotun, an bayar da belin Malami ne a kan sharuɗɗa irin waɗanda EFCC ta gindaya a baya, waɗanda suka haɗa da miƙa fasfo ɗinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262