'Yan Kasuwa Sun Rage Farashin Man Fetur ƙasa da na Matatar Dangote
- Farashin fetur ya shiga sabon yanayi bayan wasu gidajen mai sun fara sayar da lita ƙasa da N739 da matatar Dangote ke sayarwa a Najeriya
- ’Yan kasuwa da masu shigo da fetur sun rungumi dabarar rage farashi domin guje wa rasa kwastomomi a kasuwa saboda tsananin gasa
- Rahoto ya nuna cewa masu sayen mai sun koma gidajen da ke da rahusa, lamarin da ya tilasta wa sauran gidaje sauya farashi cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos – Gasar farashi a sashen man fetur ta ƙara tsananta a Najeriya bayan da wasu gidajen mai suka fara sayar da fetur ƙasa da N739 da matatar Dangote ta ayyana.
Rahotanni sun nuna cewa wannan saukin ya zo ne a daidai lokacin da gasa ke ƙaruwa tsakanin masu shigo da fetur da manyan diloli.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa rage farashin ya biyo bayan matakin da matatar Dangote ta ɗauka a watan Disamban 2025, inda ta rage farashin lita daga kusan N900 zuwa N739.
Binciken da aka gudanar a ƙarshen mako ya nuna cewa wasu gidajen mai sun fara sayar da fetur a farashi ƙasa da na MRS, wadda ita ce abokiyar hulɗa da matatar Dangote wajen aiwatar da sabon tsarin farashi.
'Yan kasuwa sun rage farashin man fetur
An gano cewa a ranar Lahadi, 11 ga Janairun 2026, wasu gidajen mai kamar NIPCO na sayar da fetur a N738 kan kowace lita, yayin da SAO ke sayarwa a N735, Akiavic kuma sun saida a N737.
A wani bayani da muka samu, wani gidan mai na AP da ke kusa da gidan man MRS a Mowe, jihar Ogun, ya saukar da farashinsa zuwa N736 kan kowace lita.
Rahotanni sun nuna cewa gidajen mai da ke yankuna ɗaya suna sa ido kan farashin juna domin kada a yi musu fintinkau a kasuwa.
Bincike ya tabbatar da cewa direbobi suna kwararowa gidajen da ke da rahusa, suna barin waɗanda ke sayarwa da tsada a yankuna.
Dalilan saukar farashin man fetur a Najeriya
Kungiyar manyan ’yan kasuwar makamashi ta bayyana cewa kudin shigo da man fetur ya kai kusan N762.38 kan kowace lita.
Duk da wannan tazara, masu shigo da fetur sun rage farashi domin su iya gogayya da MRS da ke sayar da fetur bayan saye daga matatar Dangote.
Wasu ’yan kasuwa sun bayyana cewa rage farashin ba wai saboda fetur da ake shigo da shi ya fi rahusa ba ne, illa dai wata dabara ce ta kasuwa domin jawo kwastomomi.

Source: Original
Manyan dilolin sun jaddada cewa ba su da rikici da wata matata ko ’yan kasuwa, sai dai kowa na ƙoƙarin tsayawa da kafarsa ne a kasuwa kawai.
CBN ya yi hasashen farashin fetur
A wani labarin, kun ji cewa babban bankin Najeriya na CBN ya fitar da hasashe kan yadda farashin man fetur zai kasance a 2026.

Kara karanta wannan
Sabani ya gifta tsakanin yan kasuwa da matatar Dangote kan yarjejeniyar sayen mai da sauki
Bayan lura da wasu abubuwa masu muhimmanci, bankin ya ce kudin litar man fetur a shekarar 2026 zai tsaya daga N950 zuwa kasa.
Baya ga man fetur, hasashen CBN ya nuna cewa za a samu saukar farashin kayan masarufi a Najeriya a bayanin da ya wallafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

