Hajjin 2026: Kano ta Tura Tawaga Saudiyya Domin Duba Masaukin Alhazai
- Hukumar alhazai ta Kano ta kai ziyarar duba masaukin alhazai gabanin aikin hajjin bana na shekarar 2026
- Jihar Kano na daya daga cikin biranen da ke tura mutane da yawa zuwa aikin hajji, lamarin da ke bukatar tsari
- Kusan dukkan kasashen duniya ne ke kula da mutanen kasashensu a Saudiyya domin gudanar da ayyukan hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano - Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta fara wata ziyarar duba ayyuka a hukumance zuwa birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, gabanin shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026.
Ziyarar na daga cikin matakan farko da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da cewa an tanadi dukkan muhimman abubuwan da za su taimaka wajen gudanar da aikin Hajji cikin tsari, sauƙi da kwanciyar hankali ga alhazan Jihar Kano.
Babban manufar ziyarar ita ce duba wuraren masauki da kuma hanyoyin sufuri da za a yi amfani da su yayin aikin Hajji, domin tabbatar da cewa sun cika ka’idoji, kuma sun dace da yawan alhazan da ake sa ran jihar za ta kai Saudiyya a 2026.

Source: Getty Images
Muhimman abubuwan da ake dubawa
Hakan ya haɗa da tantance nisan masauki daga Harami, yanayin gine-ginen, tsarin tsaro, tsafta da kuma dacewar motocin da za su rika kai-komo da alhazai tsakanin Makkah da sauran wuraren ibada.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Suleiman Dederi, ya fitar a ranar Lahadi a Kano, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cewarsa, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Danbappa, ne ya jagoranci tawagar ziyarar tare da shugaban hukumar, Alhaji Yusuf Lawan.
Tawagar ta duba muhimman wurare da dama domin tantance isassun kayayyaki da kuma ingancin tsarin hidimomin da aka tanada wa alhazai.
A cewar Dederi:
“Ziyarar na da nufin tabbatar da jin daɗi, kwanciyar hankali da tsaron alhazan Jihar Kano yayin aikin Hajji mai zuwa.”
Batun mazauki da zirga-zirgar alhazai
Ya kara da cewa shugabannin hukumar sun duba wuraren masaukin alhazai a Makkah tare da yin nazari kan yadda za a inganta tsarin kula da su, musamman ga tsofaffi da masu buƙata ta musamman.
A yayin ziyarar, shugabannin hukumar sun kuma gana da shugaban Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman.
Tattaunawar si ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumar jihar da ta ƙasa, da kuma magance wasu ƙalubalen aiki da kan taso a lokacin Hajji, musamman waɗanda suka shafi jigilar alhazai, masauki da bin dokokin Saudiyya.
Yadda aikin hajji ke gudana duk shekara
A bangare guda, a duk shekara, aikin Hajji na bukatar tsauraran shirye-shirye da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi daban-daban, tun daga batun biza, jiragen sama, masauki, abinci, sufuri da kuma kula da lafiyar alhazai.
Jihohi kamar Kano, wadda ke daga cikin jihohin da ke kai alhazai da yawa, na fuskantar ƙarin nauyi wajen tabbatar da cewa dukkan waɗannan abubuwa sun tafi daidai da tsari.
Saboda haka, irin wannan ziyarar duba ayyuka na taka muhimmiyar rawa wajen kauce wa matsaloli da kuma inganta kwarewar alhazai.
Asali: Legit.ng

