Gwamnatin Katsina Za Ta Fito da Ƴan Bindiga 70 daga Gidan Yari, Ta Kafa Hujjoji
- Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa sakin wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci mataki ne na tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar
- Kwamishinan tsaro Nasir Muazu ya kwatanta matakin da musayar fursunonin yaki inda ya ce an riga an saki mutane 1,000 da aka sace a baya
- Yunkurin gwamnati na sakin 'yan bindigar 70 ya haifar da babban raddi daga yan kasa, sai dai, gwamnatin Katsina ta kare kanta da hujjoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnatin Jihar Katsina ta fito fili ta bayyana dalilin da ya sanya ta fara shirin sakin mutane 70 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci da fashin daji.
Gwamnatin ta ce wannan matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin dorewar yarjejeniyar zaman lafiya da ake yi da rukunonin 'yan bindiga da ke addabar sassan jihar, musamman a yankunan karkara.

Source: Twitter
Gwamnatin Katsina za ta saki 'yan bindiga
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Nasir Muazu ne ya yi bayani game da yarjejeniyar da aka cimma da kokarin gwamnati na kiyaye hakan, in ji rahoton Vanguard.
Nasir Mua'azu ya ce za a saki 'yan bindigar ne domin ƙarfafa yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin garuruwan da abin ya shafa da kuma ’yan ta'addar da suka tuba a ƙananan hukumomi 15 na jihar.
A cewarsa, wannan yarjejeniyar ta riga ta samar da sakamako mai ƙarfi, inda aka samu nasarar sakin kimanin mutane 1,000 da aka yi garkuwa da su a baya ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Musayar fursunoni da yarjejeniyar sirri
Nasir Muazu ya kwatanta sakin waɗanda ake zargin da tsarin musayar fursunoni da kan faru a lokacin yaƙi a sassan duniya daban-daban.
Bayanin nasa na zuwa ne bayan bayyanar wata wasiƙar sirri da ta bazu a yanar gizo, inda ma’aikatar shari’a ta jihar ta nemi babban alƙalin jihar da ya sauƙaƙa sakin waɗanda ake zargin.
Wasiƙar ta bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin na tsare ne a gidan yari, yayin da wasu ke fuskantar shari’a a manyan kotuna.
Gwamnatin ta dogara da sashi na 371(2) na dokar tsarin shari’ar manyan laifuffuka ta jihar Katsina ta shekarar 2021 wajen neman wannan alfarma.
A cewar takardar, sakin waɗannan mutane shi ne babban sharaɗin da maharan suka gindaya domin ci gaba da zaman lafiya da kuma daina kai hare-hare a garuruwan jihar.

Source: Original
Damuwar jama'a da martanin gwamnati
Duk da cewa wannan matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce da damuwa tsakanin ’yan Najeriya, inda da dama ke ganin hakan na iya tauye haƙƙin waɗanda aka yi wa laifi da kuma raunana harkar tsaro, gwamnatin ta nace cewa sulhun shi ne mafita mafi sauƙi a yanzu don ceto rayukan mutane.
Kwamishina Muazu ya lissafa ƙananan hukumomi kamar Sabuwa, Safana, Kurfi, Faskari, Danmusa, Bakori, da Dutsinma a matsayin wuraren da aka samu nasarar sasantawa.
Gwamnatin ta jaddada cewa matakin nata bai saɓa wa kowace doka ba, domin tana bin matakan shari'a ne wajen neman sakin nasu.
Ta ƙara da cewa musayar fursunoni abu ne da ya taɓa faruwa a yaƙin basasar Najeriya da kuma tattaunawa da ƙungiyar Boko Haram.
Gwamnatin tana kira ga duk wanda bai gamsu ba da ya bi hanyoyin shari’a don neman ƙarin haske ko ƙalubalantar matakin.
'Yan bindiga sun farmaki 'yan Mauludi
A wani labari, mun ruwaito cewa, a yammacin ranar Juma'a 9 ga watan Janairun 2026 yan bindiga sun farmaki masu maulidi a jihar Katsina,
An tabbatar da cewa yan bindiga sun kewaye Musulman da ke bikin Maulud a Yanshantuna a Makera da ke Dutsin-Ma.
Harin ya saba wa ikirarin zaman lafiya da aka sanar bayan yarjejeniyar sulhu tsakanin shugabanni da ‘yan bindiga a karamar hukumar.
Asali: Legit.ng


