Kasafin Kudin Kihohi: Yadda Lagos ta Ninka Kano Sau Kusan 3, Sauran Jihohi 34
Kasafin kudin jihohin Najeriya na shekarar 2026 ya kara fito da bambanci mai yawa a karfin tattalin arzikin jihohi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Lagos ce ta fi kowacce jiha kasafi, inda ta zarce Kano da kusan ninki uku, duk da Kano ita ce jiha mafi yawan jama’a a Arewa.
Jerin ya nuna yadda Lagos ke ci gaba da rike ragamar kasafin kudi, yayin da jihohi da dama ke kokarin daidaita bukatu da karancin kudade a shekarar 2026.

Source: Twitter
Ga cikakken jerin jihohi 36, kowacce da karin bayani kan abin da kasafin ya fi mayar da hankali a kai.
Lagos – ₦4.24trn
Lagos ta sake zama jiha mafi karfin kasafi a Najeriya, inda ya fi karkata ga manyan ayyukan sufuri, gina hanyoyi, bunkasa tattalin arzikin zamani, kiwon lafiya da ilimi.
Haka kuma, an ware kaso mai tsoka don rage talauci da samar da ayyukan yi, musamman ga matasa.
Rivers – ₦1.85trn
Rivers ta gabatar da kasafi mai nauyi da ke mayar da hankali kan hanyoyi, wutar lantarki da bunkasa tattalin arzikin mai da iskar gas.
Gwamnatin jihar ta kuma jaddada kula da albashi da walwalar ma’aikatanta a shekarar ta 2026.
Delta – ₦1.73trn
Kasafin Delta ya fi karkata ga raya ababen more rayuwa, kula da muhalli da kuma biyan bukatun ma’aikata.
Haka zalika, an nuna damuwa kan yadda za a yi amfani da kudaden mai wajen amfanin talakawa.
Ogun – ₦1.67trn
Ogun ta mayar da hankali kan bunkasa masana’antu, gina hanyoyi da habaka ilimi.
Kasafin ya kuma nuna aniyar jawo masu zuba jari, kasancewar jihar na kusa da Lagos.
Enugu – ₦1.62trn
Enugu ta ware kudi mai yawa ga ilimi da kiwon lafiya, tare da gina hanyoyi da gyaran birane.
Gwamnatin jihar ta ce kasafin zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin yankin Kudu maso Gabas.
Akwa Ibom – ₦1.58trn
Kasafin Akwa Ibom ya fi karkata ga ayyukan wutar lantarki, noma da bunkasa matasa.
Haka kuma, an ware kaso mai yawa don ayyukan more rayuwa da rage rashin aikin yi.

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi ya nemi Tinubu ya ziyarci garin da aka yi wa jama'a yankan rago a Neja
Kano – ₦1.48trn
Kano ta rattaba hannu kan mafi girman kasafi a tarihinta, lamarin da a baya ya jawo cece-kuce daga ‘yan adawa.
Kasafin ya mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya, gina tituna, gidaje da bunkasa harkokin kasuwanci, musamman don tallafa wa dimbin al’ummar jihar, kamar yadda bayanai suka nuna.
Imo – ₦1.44trn
Imo ta tsara kasafi da ke nufin kammala manyan ayyuka da suka dade suna tsaya, tare da bunkasa tattalin arziki da tsaro.
Niger – ₦1.07trn
Kasafin Niger ya fi karkata ga aikin gona, samar da ababen more rayuwa da tsaro, musamman la’akari da fadin jihar da kuma matsalolin tsaro.
Abia – ₦1.02trn
Abia ta mayar da hankali kan tituna, kiwon lafiya da bunkasa kananan sana’o’i domin karfafa tattalin arzikin cikin gida.
Bayelsa – ₦1.02trn
Kasafin Bayelsa ya fi karkata ga raya matasa, samar da ayyukan yi da kare muhalli a yankunan mai.
Kaduna – ₦985.9bn
Kaduna ta bai wa tsaro, ilimi da bunkasa masana’antu muhimmanci, tare da kudurin kara bunkasa tattalin arzikin jihar.
Cross River – ₦961.62bn
Kasafin jihar ya mayar da hankali kan yawon bude ido, gina tituna da bunkasa aikin gona.
Edo – ₦939.85bn
Edo ta ware kudi mai yawa don samar da ayyukan yi, inganta kasuwanci da ci gaban birane.
Jigawa – ₦901.84bn
Kasafin Jigawa ya fi karkata ga aikin gona, ruwa da ilimi, domin inganta rayuwar manoma.
Katsina – ₦897.87bn
Katsina ta bai wa tsaro, noma da walwalar jama’a muhimmanci, duba da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.
Oyo – ₦892bn
Kasafin Oyo ya mayar da hankali kan tituna, ilimi, kiwon lafiya da bunkasa birnin Ibadan.
Borno – ₦890.33bn
Borno ta fi karkata ga sake gina yankunan da rikici ya shafa, taimakon jama’a da tsaro.
Ebonyi – ₦884.87bn
Ebonyi ta mayar da hankali kan noma, hanyoyin sufuri da bunkasa karkara.
Bauchi – ₦877.05bn
Kasafin Bauchi ya bai wa ilimi, kiwon lafiya da samar da ruwa muhimmanci.
Zamfara – ₦861.3bn
Zamfara ta fi karkata ga tsaro, walwalar jama’a da rage radadin talauci.
Kogi – ₦820.49bn
Kasafin Kogi ya mayar da hankali kan tituna, biyan albashi da bunkasa tattalin arziki.
Plateau – ₦817.51bn
Plateau ta bai wa tsaro, noma da yawon bude ido muhimmanci.
Anambra – ₦766.37bn
Kasafin Anambra ya fi karkata ga kasuwanci, tituna da ci gaban birane.
Sokoto – ₦758.7bn
Sokoto ta mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya da aikin gona.
Osun – ₦723.45bn
Kasafin Osun ya fi karkata ga albashi, tituna da inganta ilimi.
Benue – ₦695.01bn
Benue ta bai wa aikin gona muhimmanci, duba da matsayin ta a matsayin jihar noma da kayan abinci.
Taraba – ₦653.5bn
Kasafin Taraba ya fi karkata ga noma, hanyoyi da wutar lantarki.
Kwara – ₦644bn
Kwara ta mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya da ci gaban birane.
Kebbi – ₦642.93bn
Kasafin Kebbi ya bai wa aikin gona, ruwa da ilimi muhimmanci.
Gombe – ₦617.95bn
Gombe ta fi karkata ga noma, tsaro da walwalar jama’a.
Adamawa – ₦583.3bn
Kasafin Adamawa ya mayar da hankali kan sake gina ababen more rayuwa da taimakon jama’a.
Nasarawa – ₦545.18bn
Nasarawa ta bai wa noma, ma’adanai da hanyoyi muhimmanci.
Ondo – ₦524.41bn
Kasafin Ondo ya fi karkata ga kiwon lafiya, ilimi da wutar lantarki.
Yobe – ₦515.5bn
Yobe ta mayar da hankali kan tsaro, ilimi da tallafa wa al’ummar da rikici ya shafa.
Ekiti – ₦415.57bn
Ekiti ce ke da mafi karancin kasafi, inda aka fi bai wa ilimi, biyan albashi da kiwon lafiya muhimmanci.
Inda gwamnatin Najeriya za ta fi kashe kudi a 2026
A bangare guda, kasafin kudin shekarar 2026 da Shugaban Kasa ya gabatar ya jaddada muhimman manyan bangarori huɗu: tsaro, ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.
A cewar Bola Tinubu, waɗannan fannoni suna da alaƙa da juna, kuma su ne ginshiƙin hanyar Najeriya zuwa haɓakar tattalin arziƙi mai dorewa, kamar yadda aka wallafa a shafin X na Presidency Nigeria.
Legit ta tattaro wasu manyan bangarori da kasafin 2026 ya fi mayar da hankali a kansu, yayin da Tinubu ya bayyana muhimmancinsu ga ci gaban kasa.
Asali: Legit.ng




