Jami'an Tsaron Najeriya Sun Yi Ruwan Bama-bamai Kan 'Yan Bindiga a Kogi
- ‘Yan sanda a jihar Kogi sun bayyana nasarar da suka samu a ranar Lahadi, inda suka lallasa ‘yan bindiga da dama a jihar
- Rahoto ya bayyana yadda jami’an tsaro suka lalata kayan aikin ‘yan ta’adda, tare da fatattakarsu a wani yankin jihar Kogi
- Jihar Kogi na daga cikin jihohin Arewa da ke fama da barnar ‘yan bindiga a ‘yan shekarun bayan nan, musamman 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kogi - Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta ce an kashe ‘yan bindiga da dama tare da tarwatsa hanyoyin sadarwarsu a wani sabon samamen da aka kaddamar, sai dai ba a bayyana inda aka gudanar da aikin ba.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, William Aya, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an samu wannan nasara ne a wani aiki na hadin gwiwa da ake ci gaba da yi tsakanin ‘yan sanda da sojoji, tare da goyon bayan sashen jiragen sama na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Source: Original
A cewar Aya:
“Ayyukan samame da ake ci gaba da kai wa ‘yan bindiga a jihar Kogi da hadin gwiwar ‘yan sanda da sojoji sun haifar da gagarumar nasara.
“An fatattaki ‘yan bindiga, an rushe hanyoyin sadarwarsu, tare da kashe da dama daga cikinsu.
“Wannan aiki da ake gudanarwa cikin jajircewa, kwarewa da cikakken bin ka’ida, tare da tallafin sashen jiragen saman rundunar ‘yan sandan Najeriya ta hanyar hare-haren sama, shi ne ya kai ga wadannan nasarori.”
Al’umma ya kamata su sa ido
Rundunar ta bukaci al’umma da su kasance masu taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wanda aka gani dauke da raunukan harbin bindiga, munanan raunuka ko wasu dabi’u masu tayar da hankali zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Sanarwar ta kuma yi kira ga mazauna yankunan jihar da su mara wa jami’an tsaro baya ta hanyar bayar da sahihin bayani kan miyagun mutane da ke cikin unguwanninsu.
Ya kara da cewa:
“Tsaro hakkin kowa ne. Idan muka hada kai, za mu kyautata Najeriya.”
‘Yan sanda sun ba da lambobin ko-ta-kwana
Ya kuma fitar da lambobin dakin kula da rahotanni na rundunar, 07038329084 da 08152195982, inda al’umma za su iya kai rahoton duk wani motsi a kowane yanki na jihar.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kara tsananta ayyukan ta’addanci a wasu sassan jihar Kogi a ‘yan watannin nan.
Tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba, an kai hare-hare kan coci biyu, lamarin da ya sa Sarkin Kabba, Obaro na Kabba, Oba Solomon Owoniyi, tare da hadin gwiwar CAN, suka haramta dukkan harkokin addini a yankin.
A ranar Asabar, mazauna Zango da ke Lokoja sun ruwaito jin harbe-harben bindiga a wurare daban-daban, lamarin da ya kai ga sace mambobi hudu na iyali daya. Daga bisani, ‘yan bindigar da suka tsere sun saki wata tsohuwa da kuma wani yaro.
Matakin da gwamnatin Kogi ke dauka kan magance tsaro
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Kogi ta yi martani kan harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wani coci da ke jihar.
Gwamnatin ta ce ta kara tsaurara sa ido da sintiri tare da kaddamar da farautar ’yan bindigarln da suka kai hari a cocin Cherubim and Seraphim da ke Ejiba, karamar hukumar Yagba ta Yamma ta jihar.
Jaridar Vanguard ta ce kwamishinan yada labarai da harkokin sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya bayyana hakan.
Asali: Legit.ng


