Katsina: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari ana tsaka da Bikin Maulidi, Sun Tafka Barna
- A yammacin ranar Juma'a 9 ga watan Janairun 2026 yan bindiga sun farmaki masu maulidi a jihar Katsina
- An tabbatar da cewa yan bindiga sun kewaye Musulman da ke bikin Maulud a Yanshantuna a Makera da ke Dutsin-Ma
- Harin ya saba wa ikirarin zaman lafiya da aka sanar bayan yarjejeniyar sulhu tsakanin shugabanni da ‘yan bindiga a karamar hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Duk da zaman sulhu da ake yi a jihar Katsina, yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare kan al'umma.
Karamar hukumar Dutsin-Ma na daga cikin yankunan da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da maharan.

Source: Original
Rahoton Bakatsine ya ce yan bindiga sun kai wani hari a jihar Katsina yayin bikin Maulidi a ranar Jum'a 9 ga watan Janairun 2026.
Yadda Katsina ke fama da harin yan bindiga
Jihar Katsina na daga cikin jihohi a Arewa maso Yamma da ke fama da matsalolim hare-haren yan bindiga a Najeriya.
Wannan lamari na tayar da hankula duba da irin zaman sulhu da wasu yankuna ke yi da maharan domin samun zaman lafiya.
Duk da haka, wasu na ganin sulhun na da muhimmanci saboda zai samar da kwanciyar hankali da ba manoma damar gudanar da harkokin noma.
Yan bindiga sun kai hari kan masu Maulidi
Majiyar ta ce a lamarin ya faru ne a yammacin jiya Juma'a 9 ga watan Janairun 2025 a Yanshantuna, Makera Ward, Dutsin-Ma.
Yan bindiga sun kewaye jama’a, sun kwace wayoyi, kuɗi, da kuma sace kayan shagon caji yayin farmakin.
Wannan lamari ya ci karo da ikirarin zaman lafiya da jami’ai suka yi bayan yarjejeniyar sulhu da aka ce an cimma tsakanin shugabannin al’umma da ƙungiyoyin ‘yan bindiga.
Yanzu haka, mazauna yankin na neman bayani kan matakan sa ido da tilastawa da aka tanada domin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiyar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Yan Maulidi sun kubuta daga yan bindiga
Wannan na zuwa ne bayan wasu matafiya zuwa bikin Maulidi sun fada komar yan bindiga a jihar Plateau lamarin da ya tayar da kura.
Mutanen da ke kan hanyar zuwa wurin taron Mauludi da 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a jihar , sun shaki iskar 'yanci daga baya.
Majiyoyi sun bayyana cewa mutanen sun shaki iskar 'yanci ne bayan sun shafe kwanaki 20 a hannun 'yan bindiga.
Tun da farko, 'yan bindigan dai sun bukaci a ba su makudan kudade kafin su sako mutanen wadanda suka hada da mata da maza.
Yan bindiga sun hallaka masu Maulidi
Mun ba ku labarin cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki ana tsaka da gudanar da bikin Mauludi a ƙauyen Kusa na jihar Katsina.
Ƴan bindigan waɗanda suka buɗewa mutanen da ke wurin wuta, sun halaka mutane masu yawa tare da raunata wasu.
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da aukuwar harin inda ta ce tana cigaba da gudanar da bincike domin cafke maharan.
Asali: Legit.ng

