Bayan Zama da Kwankwaso a Asirce, Abba Kabir Zai Hadu da Tinubu a Faransa

Bayan Zama da Kwankwaso a Asirce, Abba Kabir Zai Hadu da Tinubu a Faransa

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Rabiu Kwankwaso a asirce a Kano, kafin ya tafi Faransa
  • Rahoto ya ce gwamnan na kokarin shawo kan Kwankwaso ya koma APC, amma tsohon sanatan ya kafe
  • Duk da sauya shekarsu zuwa APC, magoya bayan Kwankwasiyya sun tsaya daram da Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da uban gidansa a siyasa a asirce, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Majiyoyi suka ce an yi ganawar a wani taron sirri da aka yi a gidansa da ke hanyar Miller, Kano, a ranar Talata 6 ga watan Janairun 2026.

Abba Kabir ya gana da Tinubu a Faransa
Sanata Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir a taro. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Abin da Abba ya nema daga Kwankwaso

Bayan wannan ganawa, gwamnan ya tashi zuwa kasar Faransa a ranar Juma’a 11 ga watan Janairun 2026 domin ganawa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Gwamna Abba ya yi alkawarin kin yi wa Kwankwaso butulci

Rahoton ya nuna cewa gwamnan ya nemi ganin Kwankwaso ne domin yin kokarin karshe na shawo kansa ya shiga jam’iyyar APC bisa umarnin da ake zargin shugaban kasa ya bayar.

Majiyoyi sun ce Gwamna Abba Yusuf ya isa gidan Kwankwaso da tsakar dare, tare da wani mai shiga tsakani da ake kira Sarkin Gobir inda suka zo cikin mota ta kashin kansu.

Ko da yake an ce ganawar ta dauki fiye da awa guda, alamu sun nuna cewa gwamnan bai samu nasarar shawo kan Kwankwaso ya sauya matsayinsa ba.

Washegari bayan ganawar, Kwankwaso ya yi jawabi ga magoya bayansa a gidansa, inda ya bayyana karara cewa ba shi da farashi a siyasa.

Ya ce:

“Da fari dai, mun san cewa cin amana ba abu ne mai kyau ba. Kowa ya san yadda waccan jam’iyya ke rasa goyon bayan jama’a, musamman dangane da tsaro da tattalin arziki.
“A Najeriya ana cewa kowa na da farashi. Idan kuna neman wanda ba shi da farashi, to ku zo wurin Rabiu Kwankwaso."
Bayan ganawa da Kwankwaso, Abba ya je wurin Tinubu a Faransa
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Halin da ake ciki a siyasar Kano

Majiyoyi sun ce shirin gwamna Abba Kabir na sauya sheka ya fuskanci babban kalubale bayan da manyan APC suka ga irin martanin da jama’a suka nuna a Kano.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso da Abba Kabir ke shirin ɓaɓewa bayan shafe shekaru 40 tare

Duk da cewa ‘yan majalisa na NNPP a matakin jiha da kasa, da kuma shugabannin kananan hukumomi, suna bin gwamnan zuwa APC, mafi yawan magoya bayan jam’iyyar a matakin kasa sun tsaya tsayin daka tare da Kwankwaso.

Wata majiya ta ce:

“Shugabannin APC na sa ido sosai kan abin da ke faruwa a Kano. Magoya bayan Kwankwasiyya sun bayyana a fili cewa suna tare da Kwankwaso.”

Ta kara da cewa Rabiu Kwankwaso na kara samun goyon baya daga jama’a a fadin jihar, inda ta ce idan Abba Yusuf ya koma APC.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Tinubu na nan daram kan ganin Kwankwaso ya shiga APC, shi ya sa ake kara matsin lamba na karshe domin shawo kansa ya dawo jam'iyya mai adawa.

Abin da Abba zai 'fadawa' Tinubu

An ce gwamnan zai gabatar wa shugaban kasa rahoto kan ganawarsa da tsohon ubangidansa, sannan su tsara hanyar ci gaban jam’iyyar bayan sauya shekar gwamnan.

A halin yanzu, manyan shugabannin APC a Kano, ciki har da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, shugaban APC na jihar Abdullahi Abbas, da Nasiru Gawuna da Murtala Garo, sun dawo Najeriya bayan hutun karshen shekara da aikin Umrah.

Kara karanta wannan

Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda

Ana sa ran gwamnan zai sanar da sauya shekar sa zuwa APC bayan ya kammala tuntuba da shugabannin jam’iyyar a jihar.

Kwankwaso ya zargi Abba da cin mana

A wani labarin, Sanata Rabiu Kwankwaso ya gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf kan shirin komawa jam'iyyar APC, inda ya bayyana hakan da 'cin amana'.

Kwankwaso ya ce lallai akwai bukatar wadanda ke shirin barin NNPP zuwa APC a Kano su biya 'yan Kwankwasiyya wahalar da suka yi masu.

Majalisar dokokin jihar Kano dai ta amince da sauya shekar gwamnan zuwa APC domin kaucewa fadawa tarkon shari'ar da ta faru a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.