Hajji: Gwamnatin Tinubu Za Ta Tatsi Harajin N5.4bn, an Fadi Yadda Maniyyaci Zai Biya

Hajji: Gwamnatin Tinubu Za Ta Tatsi Harajin N5.4bn, an Fadi Yadda Maniyyaci Zai Biya

  • Rahoto ya nuna gwamnatin tarayya na shirin samun biliyoyin Naira daga alhazan Najeriya na Hajjin 2026 ta hanyar kudin hidima na 2%
  • Kungiyar Independent Hajj Reporters (IHR) ta ce kowane maniyyaci zai biya kimanin N136,417, wanda za a tura kai tsaye zuwa Babban Bankin Najeriya
  • Ta bukaci gwamnati da CBN su bayyana yadda ake amfani da kudin, tare da rokon Majalisar Tarayya ta yi bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya na shirin samun kusan Naira biliyan 5.4 daga maniyyatan Najeriya.

Harajin zai fito ne daga maniyyata da za su halarci aikin Hajjin shekarar 2026, sakamakon wani kudin hidima na dole da aka kakaba musu.

Gwamnatin Tinubu za ta samu harajin N5.4bn daga maniyyata aikin hajji
Shugaba Bola Tinubu yayin jawabi a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Harajin da kowane maniyyaci zai biya a Najeriya

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Independent Hajj Reporters (IHR), wata kungiya mai sa ido kan gaskiya da rikon amana a harkokin aikin Hajji, ta fitar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Sanatan Najeriya ya gina danƙareren gida, talakawa sun masa rubdugu a intanet

Majiyoyi sun bayyana cewa kowanne maniyyaci na shekarar 2026 zai biya kudin hidima na 2% kai tsaye zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN).

Kungiyar ta ce, duba da cewa kudin aikin Hajji na 2026 ya kai kimanin Naira miliyan 7.6 ga kowane mutum, wannan karin haraji na nufin maniyyaci zai biya kusan N136,417 a matsayin kudin hidima.

IHR ta kara da cewa, idan aka yi la’akari da adadin maniyyata 40,000 da aka ware wa jihohi daban-daban, jimillar kudin da CBN zai tara na iya kaiwa tsakanin Naira biliyan 5.3 zuwa Naira biliyan 5.4.

A bangaren kudin kasashen waje kuwa, rahoton ya nuna cewa kowane maniyyaci zai biya kusan dala $92.46, wanda ya kai kimanin dala miliyan 3.7, adadin da ya fi na shekarar 2025 inda aka karbi $90.

An fadi awan haraji da kowane maniyyaci zai biya a bana
Shugaban hukumar NAHCON a Najeriya, Farfesa Abdullahi Pakistan. Hoto: NAHCON.
Source: Facebook

Harajin gwamnati kan maniyyata ya jawo magana

Kungiyar ta bayyana cewa an kakaba wannan kudin ne musamman domin sauya kudade zuwa asusun bankin Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da ke kasar Saudiyya.

IHR ta tuna cewa tun a watan Oktoban 2025 ta nemi gwamnati da ta janye wannan kudin, tana mai cewa karin kudin na kara wa ‘yan kasa nauyi a lokacin da suke fuskantar tsadar rayuwa daga hukumomi daban-daban.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Sanarwar ta ce:

“Tattara irin wannan makudan kudade na nuna cewa aikin Hajji ya zama wata babbar hanyar samun kudaden shiga ga gwamnati, ba wai bangaren addini kadai ba.”

Duk da tattaunawa da ake yi, har yanzu CBN ko gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba su sanar da soke ko sauya wannan tsari ba, inda majiyoyi suka ce kudin na nan daram, cewar Daily Post.

Kungiyar ta bukaci gwamnati da Babban Bankin Najeriya su fito fili su bayyana dalilin wannan kudin tare da yadda ake kashe shi, sannan ta nemi Majalisar Tarayya ta sa ido.

NAHCON ta rage adadin kujerun Najeriya

A baya, kun ji cewa Najeriya za ta samu kujeru 66,910 kacal a aikin Hajjin 2026 bayan Saudiyya ta rage adadin da aka saba ba ta.

Hukumar aikin hajji ta kasa, NAHCON ta bayyana dalilin da ya sa kasa mai tsarki daukar matakin a 2026.

An sanar da sauyin ne a taron da hukumar ta yi da jihohi don tattauna batun rage kudin Hajji da aka ce a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.