Sanatan Najeriya Ya Gina Danƙareren Gida, Talakawa Sun Masa Rubdugu a Intanet

Sanatan Najeriya Ya Gina Danƙareren Gida, Talakawa Sun Masa Rubdugu a Intanet

  • Bidiyon Ministan Abuja, Nyesom Wike, yana yabon katafaren gidan Sanata George Sekibo ya bazu, ya haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta
  • Wasu sun kare tarin dukiyar da Sanatan na jihar Rivers ya mallaka, yayin da wasu ke kallon lamarin a matsayin nuna bambancin tattalin arziki a Najeriya
  • Ra’ayoyin jama’a sun rabu tsakanin yabo, suka kan ‘yan siyasa, da kira ga a rika biyan bukatun al’ummar da suka zabi 'yan siyasa maimakon gina gidaje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers – Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kai ziyara tare da yabawa katafaren gidan Sanatan Rivers, George Sekibo, lamarin da ya tayar da ce-ce-ku-ce.

Bidiyon, wanda aka dauka a Rivers, ya nuna yadda Wike ke bayyana girma da kyawun gidan Sanatan, abin da ya sa jama’a da dama suka fara tofa albarkacin bakinsu kan dalilin nuna irin wannan dukiya a kasar da ke fuskantar kalubalen tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Gidan Sanata George Sekibo a Rivers
Katafaren gidan Sanata George Sekibo da ke Rivers. Hoto: @PH_Socials
Source: Twitter

Rahoton Arise News ya nuna cewa tun bayan bullar bidiyon, ra’ayoyi mabambanta suka fara bayyana, inda wasu ke kallon lamarin a matsayin alamar nasara, yayin da wasu ke ganin yana nuna matsalar da Najeriya ke fuskanta.

Wike ya ziyarci katafaren gidan Sanata Sekibo

A cikin bidiyon, an ji Wike yana yaba wa Sanata George Sekibo kan girman gidansa da yadda aka gina shi, yana mai bayyana shi a matsayin abin alfahari.

Masu martani sun yi korafi da cewa yabon ne ya zama silar da jama’a suka mayar da hankali kan rayuwar jin dadi da wasu ‘yan siyasa ke yi.

Gidan Sanata George Sekibo a Rivers
Wajen da ruwa ke gudana a gidan Sanata George Sekibo. Hoto: @PH_Socials
Source: Twitter

Wasu masu sharhi sun ce babu laifi mutum ya mallaki dukiya idan ta halal ne, suna cewa shiga siyasa ba za ta hana mutum samun arziki ba.

Sai dai a daya bangaren, wasu sun ce irin wannan yabo daga manyan jami’an gwamnati yana iya kara fusata jama’a, musamman a lokacin da mutane da dama ke fama da tsadar rayuwa, rashin ayyukan yi, da karancin abubuwan more rayuwa.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya nemi Tinubu ya ziyarci garin da aka yi wa jama'a yankan rago a Neja

Talakawa sun dura kan Sanata Sekibo

A shafin X, wani mai aiki da suna @udeochusp ya bayyana cewa kasar nan na hannun ‘yan siyasa, yana nuna rashin amincewa da yadda ake tafiyar da al’amura.

Shi ma @Lawdiasa ya ce ‘yan siyasar Najeriya sun fi maida hankali ne kan tara dukiya a kansu, maimakon kula da walwalar jama’a. Wannan ra’ayi ya samu goyon bayan wasu da ke ganin siyasa ta koma hanyar tara arziki kawai.

A wani salo na daban, @ijeoma_nwafor ta yi tsokaci kan tsarin ginin gidan, tana cewa duk da girman sa, rashin tsari da yawan kayan daki sun rage masa armashi.

Haka kuma, @Everypolitics1 ya kwatanta yanayin ginin da halin da Rivers ke ciki, yana cewa jihar na kuka da rashin hanyoyi, asibitoci da makarantu, amma ana shagalta da yabon manyan gidaje.

A nasa bangaren, @steve_oru ya ce matsalar ba ta ‘yan siyasa kadai ba ce, har da talakawan da ke yabonsu ba tare da neman su sauke nauyin da ke kansu ba.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Dalilan da suka jawo sabon rikici tsakanin Fubara da Wike

Rikicin siyasa ya dawo sabo a Rivers

A wani labarin, kun ji cewa sabon rikici ya barke a jihar Rivers, inda 'yan majalisar jihar suka fara yunkurin tsige gwamna Siminalayi Fubara.

Matakin na zuwa ne bayan sake samun rashin fahimta tsakanin gwamna Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike bayan musu sulhu.

Masu sharhi sun bayyana cewa rashin cika wasu alkawura da batun kasafin kudin 2026 ne suka sake jawo rikicin da ya barke a Rivers.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng