Halin da Masu Zuwa Mauludi Suke Ciki bayan Kwashe Kwanaki a Hannun 'Yan Bindiga a Plateau
- Mutanen da ke kan hanyar zuwa wurin taron Mauludi da 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a jihar Plateau, sun shaki iskar 'yanci
- Majiyoyi sun bayyana cewa mutanen sun shaki iskar 'yanci ne bayan sun shafe kwanaki 20 a hannun 'yan bindiga
- Tun da farko, 'yan bindigan dai sun bukaci a ba su makudan kudade kafin su sako mutanen wadanda suka hada da mata da maza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Jami'an tsaro sun ceto matafiya 28 da 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a ranar 21 ga watan Disamban 2025 a jihar Plateau.
'Yan bindigan dauke da makamai sun sace matafiyan ne a kauyen Zak da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta Jihar Plateau.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa wani jagoran matasa a karamar hukumar Wase, Sap'i Sambo ya tabbatar da ceto mutanen.

Kara karanta wannan
Babbar magana: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari 'wurin shakatawa' na gwamnatin tarayya
'Yan bindiga sun sace mutane a Plateau
Mutanen da aka sace sun haɗa da maza, mata da yara, kuma suna kan hanyarsu ne ta zuwa ƙauyen Sabon Layi, a cikin wannan gundumar ta Bashar, domin halartar taron Mauludi, lokacin da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su.
Bayan faruwar lamarin, masu garkuwar sun tuntuɓi ’yan uwan waɗanda aka sace, inda suka buƙaci kudin fansa na Naira miliyan 1.5 daga kowane mutum.
’Yan uwan sun bayyana cewa ba su da ikon biyan wannan kuɗi, suka kuma roki masu garkuwar da su sake su.
Yadda 'yan bindiga suka canza kudin fansa
Daga baya, masu garkuwar sun rage bukatar kudin fansar zuwa Naira miliyan 30 gaba ɗaya, amma suka kara da sharadin a ba su sababbin babura guda uku.
A ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026 kuma, iyalan waɗanda aka sace sun ce masu garkuwar sun sake sauya sharuddan, inda suka buƙaci Naira miliyan 1.5 da sabon babur guda ɗaya ga kowane mutum kafin sakin su.
An ceto masu zuwa Mauludi a Plateau
Da yake tabbatar da sakin mutanen, Sapi’i Sambo ya bayyana cewa:
“Jami’an DSS ne suka kira mu da daddare suka sanar da mu cewa sun ceto waɗanda aka sace. Wannan labari ya sanya farin ciki a ko’ina cikin Wase, domin mutane sun shiga fargaba kan abin da zai faru idan ba a cika sharuddan ba. Muna matukar farin ciki da wannan cigaban.”

Source: Original
Haka kuma, wani uba daga ƙauyen Zak wanda ɗansa na cikin waɗanda aka sace, Dauda Ibrahim, ya tabbatar da sakin mutanen, yana mai cewa:
“Jami’an tsaro sun sanar da mu cewa an saki ’ya’yanmu kuma a halin yanzu suna cikin garin Bashar. Muna godiya ga Allah Maɗaukaki da kuma jami’an DSS.”
A bayanan da aka samu zuwa yanzu, sai dai ba a tabbatar ko an biya kuɗin fansa ba, amma iyayen sun ce ba su biya ko sisi ba.
Mutanen dai da aka sace sun shafe kwanaki 20 a hannun masu garkuwa da mutane kafin a sake su.
Jami'an tsaro sun ceto mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasarar ceto mutanen da 'yan bindiga suka sace a Zamfara.
Jami'an tsaron sun samu nasarar ceto dukkan mutane 20 da aka sace daga kauyen Dunfawa da ke yankin Moriki, a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Hakazalika, jami'an tsaron sun yi raga-raga da 'yan bindigan da suka sace mutanen wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

