Sheikh Isa Pantami Ya Yi Magana kan Rade Radin Cewa zai Auri Aisha Buhari

Sheikh Isa Pantami Ya Yi Magana kan Rade Radin Cewa zai Auri Aisha Buhari

  • Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya fito karara ya musanta rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin auren Aisha Buhari
  • Tsohon minista, Pantami ya jaddada cewa marigayi Muhammadu Buhari uba ne a gare su, yayin da matarsa Aisha Buhari take a matsayin uwa
  • Wasu jama’a sun yi martani karkashin sakonsa, suna bayyana cewa jita-jitar ba ta da tushe kuma gaskiya ta riga ta bayyana bayan ya yi bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi karin haske kan rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke alakanta shi da shirin auren uwargidan marigayi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari.

Pantami, wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Buhari, ya bayyana rade-radin a matsayin kirkirarren labari mara tushe, yana mai cewa abin ya ba shi mamaki matuka.

Kara karanta wannan

Jarumar fim da bidiyon tsiraicinta ya bazu a intanet ta yi magana

Sheikh Isa Ali Pantami da Aisha Buhari
Sheikh Isa Ali Pantami da Aisha Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Pantami ya wallafa sakon karyata shirin auren ne a Facebook bayan jita-jitar ta bazu sosai a kafafen sada zumunta, lamarin da ya haifar da muhawara da martani daga jama’a da dama a fadin kasa.

Isa Pantami zai auri Aisha Buhari?

A cikin martaninsa, Pantami ya bayyana a fili cewa babu wata hujja ko dalili da zai sa irin wannan jita-jita ta samu wuri a zukatan jama’a.

A cewarsa, marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance uba ne ga dukkan mutanen da suka yi aiki a gwamnatinsa, kuma wannan matsayi ne da ba zai taba canzawa ba.

A Sakon da shafin Green Barge Reporters ya fitar, Pantami ya jaddada cewa Aisha Buhari uwa ce a gare shi da sauran wadanda suka yi aiki karkashin marigayi shugaban kasar.

Martanin jama’a a yanar gizo

Bayan Pantami ya wallafa martaninsa, jama’a da dama sun yi tsokaci a karkashin sakonsa, suna bayyana ra’ayoyinsu game da lamarin.

Kara karanta wannan

Da gaske Sheikh Pantami zai auri Aisha Buhari? An samu bayanai

Nafi’u Zannan Zurmi ya ce mutane da dama sun riga sun fahimci cewa labarin jita-jita ne kawai da ke yawo ba tare da tushe ba.

Shi ma Muhammad Jibril Kaura ya bayyana cewa Pantami mutum ne mai mutunci, kuma ya dade da daukar Aisha Buhari a matsayin uwa, ba wai wata alaƙa ta daban ba.

Saidu Sulaiman S S ya yabawa Pantami bisa yadda ya yi shiru tun farko, yana mai cewa shiru a wasu lokuta alheri ne, musamman idan ana fuskantar rade-radi marasa tushe.

Aisha Buhari da Muhammadu Buhari
Aisha Buhari da marigayi Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Haka kuma, Hba Nuhu ya ce bayanin Pantami ya taimaka wajen fayyace gaskiya da kawar da duk wani rudani da ke cikin zukatan jama’a.

Matsayar Aisha Buhari kan sake aure

A wani rahoton, kun ji cewa Aisha Buhari ta taba bayyana matsayarta a fili game da batun sake aure bayan rasuwar mijinta, Muhammadu Buhari.

Uwargidan tsohon shugaban kasar ta ce ba ta da shirin sake aure, domin ta zabi mayar da hankali ne wajen kula da ‘ya’yanta da jikokinta a gida.

Legit Hausa ta rahoto cewa Aisha Buhari ta bayyana haka ne a littafin tarihin rayuwar marigayi Muhammadu Buhari da aka fitar a karshen 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng