Zargin Ta’addanci: CAN Ta Magantu kan Gwamna Bala bayan Shafa Masa Kashin Kaji

Zargin Ta’addanci: CAN Ta Magantu kan Gwamna Bala bayan Shafa Masa Kashin Kaji

  • Kungiyar Kiristoci, CAN a jihar Bauchi a yau Juma'a ta yi martani kan batun zargin Gwamna Bala Mohammed kan hannu a ta'addanci a Najeriya
  • CAN ta ce babu wata hujja da ke danganta Gwamna Bala da daukar nauyin ta’addanci da ake magana a kai a kwanakin
  • Mabiya addinin Kiristan sun jaddada cewa gwamnan shugaba ne mai adalci, juriya da girmama addinai a jihar Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi magana kan zargin ta'addanci da ake yi wa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Kungiyar ta bayyana cewa, duba da irin zaman lafiyar da ake morewa a jihar, babu wani abu da ke alakanta Gwamna Bala da daukar nauyin ta’addanci.

Kungiyar CAN ta wanke Gwamna Bala kan zargin ta'addanci
Gwamna Bala Mohammed da shugaban CAN a Bauchi, Abraham Damina Dimeus. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Facebook

CAN ta wanke Gwamna Bala daga zargin ta'addanci

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi zazzafan martani kan jita jitar Gwamna Bala zai koma ADC

Hakan na cikin wata sanarwa da Shugaban CAN na jihar, Rabaran Dr. Abraham Damina Dimeus, da Sakataren kungiyar, Rev. Matthew Wakili Laslimbo, suka sanya wa hannu, cewar Tribune.

Kungiyar ta jaddada cewa mazauna Bauchi sun shaida irin kokarin da gwamnan ke yi wajen magance matsalolin tsaro, inda mutane ke rayuwa cikin zaman lafiya ba tare da bambancin addini ko kabila ba.

CAN ta bayyana mamakinta kan zarge-zargen, tana mai cewa ba su da tushe, cike suke da sharri da bata sunan Jihar Bauchi.

Sanarwar ta ce Gwamna Bala Mohammed ya nuna jajircewa wajen inganta zaman lafiya tsakanin addinai, tallafa wa cibiyoyin Kiristoci, adalci, kare hakkin dan Adam, da kuma tabbatar da tsaro a jihar.

Gwamna ya musanta alakanta shi da ta'addanci
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: @SenBalaMohammed.
Source: Facebook

Ta'addanci: CAN ta soki masu zargin Gwamna Bala

CAN ta ce, a wurin Kiristoci, zarge-zargen na da alaka da siyasa, suna kama da tsanantawa da yunkurin haddasa rikici domin cimma bukatun siyasa na wasu.

Ta kara da cewa zarge-zargen karya ne, kuma wasu ‘yan siyasa daga wajen jihar tare da wasu marasa gaskiya a ciki ne ke haddasa su domin bata sunan Bauchi da Gwamnanta.

Kara karanta wannan

Majalisar Rivers ta lissafo zunuban Fubara 11 yayin take shirin tsige shi

Kungiyar ta ce:

“A matsayimu na Kiristoci masu kishin hadin kai da zaman lafiya tsakanin addinai, muna Allah-wadai da wadannan zarge-zarge, kuma za mu hana duk wani yunkuri da zai iya rushe zaman lafiyar da muke morewa a Bauchi.”

Kungiyar ta bukaci jama’a su yi watsi da wadannan zarge-zarge tare da goyon bayan Gwamnan yayin da yake ci gaba da yi wa jihar hidima da kwazo.

CAN ta bayyana cewa Kiristoci a Bauchi sun fi jin kariya a karkashin mulkin Gwamna Bala Mohammed fiye da kowane lokaci a tarihin jihar.

Kungiyar ta kammala da cewa:

“A wurinmu, Mai Girma Gwamna Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ba ya goyon bayan ‘yan ta’adda, kuma ba ya daukar nauyin ta’addanci ta kowace hanya.”

PDP ta karyata cewa Gwamna zai koma ADC

An ji cewa jam’iyyar PDP ta yi karin haske game da jita-jitar cewa Gwamna Bala Mohammed zai koma ADC a Bauchi.

Jam'iyyar ta karyata rade-radin cewa Gwamnan na shirin ficewa daga PDP da ake ta yadawa a kafofin sadarwa.

Shugaban PDP na jihar, Sama’ila Burga ya musanta zargin ne a taron masu ruwa da tsaki da suka tabbatar da cikakken goyon baya ga gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.