Fashewar Batirin Sola Ya Jawo Mummunar Gobara a Kasuwa a Katsina

Fashewar Batirin Sola Ya Jawo Mummunar Gobara a Kasuwa a Katsina

  • Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta kai dauki bayan barkewar gobara a Haiba Plaza da ke gaban kasuwar a karamar hukumar Malumfashi a Katsina
  • Binciken farko ya nuna cewa fashewar batirin sola a wani shago ne ya haddasa gobarar, inda ta lalata kayayyaki masu darajar miliyoyin Naira
  • Rahotanni sun nuna duk da barnar da gobarar ta yi, ba a samu asarar rai ko jikkatan mutane ba saboda wasu matakai da aka dauka da gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar agajin gaggawa ta NEMA, ta ofishin ayyukanta na Kaduna, ta kai dauki cikin gaggawa bayan barkewar wata gobara a Haiba Plaza da ke a wata a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun tabbatar da cewa gobarar ta faru a kasuwar ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Da gaske Sheikh Pantami zai auri Aisha Buhari? An samu bayanai

Shagunan da suka kone a Kastina
Mutanen da suka kai dauki wajen kashe gobara a Katsina. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

Hukumar bayar da agaji ta NEMA ta yi karin bayani game da yadda aka kashe wutar a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.

Batirin sola ya tayar da gobara a Katsina

Binciken farko da hukumomi suka gudanar ya nuna cewa fashewar batirin sola da ake amfani da shi a wani shago ne ya haddasa gobarar.

Rahotanni sun bayyana cewa fashewar batirin ta janyo wuta mai karfi wadda ta kama shaguna masu yawa a cikin ginin Haiba Plaza.

Akalla shaguna 13 ne aka tabbatar sun lalace sakamakon gobarar, inda aka rasa kayayyaki da kadarori masu tarin yawa.

Shagunan da suka kone sun hada da wuraren ajiyar kaya, wuraren saye da sayarwa, da sauran wuraren sana’o’i, abin da ya jefa ’yan kasuwa cikin babbar asara.

Duk da girman barnar dukiya, rahotanni sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko jikkata ba, saboda saurin kai dauki da kuma wayar da kan jama’a a yankin.

Kara karanta wannan

NLC ta yi wa Tinubu barazana saboda a dakatar da dokokin haraji

An yi hadaka wajen kashe gobarar

Aikin kashe gobarar ya gudana ne karkashin jagorancin NEMA, tare da hadin gwiwar hukumar kashe gobara ta karamar hukumar Malumfashi da ta Kafur.

Haka kuma, rundunar ’yan sanda ta kasa da hukumar NSCDC sun taka rawar gani wajen tabbatar da tsaro da daidaita jama’a a wurin.

Kungiyoyin agajin na addini, ciki har da JIBWIS da JNI, sun bayar da gudumawa wajen taimakon gaggawa da kula da wadanda abin ya shafa.

Wajen da aka yi gobara a Malumfashi
Yadda gobara ta kama a Malumfashi a Katsina. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

An bayyana cewa jami’an kananan hukumomi sun kasance a wurin domin saukaka ayyukan ceto da hada kai tsakanin bangarori daban-daban.

Shugaban karamar hukumar Malumfashi, Hon. Muntari Abdullahi City, ya halarci wurin da kansa, inda ya yaba da yadda hukumomi suka hada kai wajen dakile gobarar cikin lokaci.

Gobara ta cinye shaguna a Sokoto

A wani labarin, kun ji cewa mummunar gobara ta tashi a wata kasuwa a jihar Sokoto, inda wutar ta cinye shaguna da dama.

Kara karanta wannan

Nijar da kasashe 2 sun ci bashin wutar lantarkin N25bn a Najeriya sun gaza biya

Rahotanni sun nuna cewa baya ga shaguna, gobarar ta lakume motoci da dama, lamarin da ya jawo asarar miliyoyin Naira.

'Yan kasuwar da abin ya shafa sun bayyana cewa suna cikin damuwa sosai, tare da rokon gwamnatin Sokoto ta kai musu dauki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng