Za a Karrama Sarkin Musulmi da Gwamnoni 4 da Digirin Digirgir a Najeriya
- Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero a Kebbi za ta karrama Gwamna Nasir Idris da digirin girmamawa
- Sarkin Musulmi, Ooni na Ife da gwamnonin jihohin hudu na cikin manyan da za a ba digirin girmamawa na musamman
- Jimillar dalibai 7,221 daga zangon karatu 13 za su karɓi digiri da shaidun kammala karatu a taron karramawar a jihar Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero (AFUSTA) a Jihar Kebbi za ta ba da digirin girmamawa ga manyan mutane a Najeriya.
Jami'ar za ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da digirin girmamawa.

Source: Facebook
Gwamnoni 4 za su samu digirin girmamawa
Rahoton Leadership ya ce sauran sun hada da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, da kuma gwamnonin jihohin Sokoto, Zamfara da Imo.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Danshehu Bagudu Gwadangaji, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a dakin taro na jami’ar da ke Aliero.
Farfesa Danshehu ya ce wadannan fitattun ‘yan Najeriya za su karɓi digirin girmamawar ne a yayin taron yaye dalibai na farko da jami’ar ke shiryawa a hade, na zangon karatu na 2010/2011 da kuma 2023/2024, wanda aka shirya yi a ranar Asabar, 10 ga Janairun 2026.
A cewarsa, shugabancin jami’ar ya yanke shawarar ba wadannan mutane digirin ne bisa la’akari da jajircewarsu a fagen shugabanci, hidima da kuma gudunmawar da suka bayar ga ci gaban jihohinsu, kasa baki daya da kuma bil’adama.
Ya kara da cewa wadannan shugabanni masu daraja da sarakunan gargajiya sun taka rawar gani wajen inganta shugabanci nagari, gina zaman lafiya, bunkasa ilimi da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a sassan kasar nan.

Source: Facebook
Daliban da za su karbi shaidar kammala karatu
Farfesa Danshehu ya kuma bayyana cewa dalibai guda 7,221 daga zangon karatu 13 daban-daban ne za su samu digiri, difloma da shaidun kammala karatu a wannan taron yaye dalibai, wanda ya bayyana a matsayin tarihi ga jami’ar.
Ya ce taron yaye daliban zai zama wani muhimmin al’amari a tarihin jami’ar AFUSTA, kasancewar shi ne na farko tun bayan kafuwar jami’ar, kuma ya nuna yadda jami’ar ke ci gaba da taka rawa wajen samar da kwararru masu amfani ga kasa.
Digirin PhD: Masarautar Kano ta taya Sanusi II murna
A baya, kun ji cewa jami'ar SOAS da ke birnin Landan ta yaye Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II bayan kammala digiri na uku.
Masarautar Kano ta fitar da sakon taya murna ga Mai Martaba Sarki Sanusi II bisa wannan nasara da ya samu a rayuwarsa wanda zai amfani al'umma baki daya.
Tawagar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da sauran manyan mutane sun halarci bikin a Landan domin halartar bikin yaye Sarki wanda ya karbi shaidar digirin digirgir.
Asali: Legit.ng

