Kaduna: Babban Basarake Ya Yi Bankwana da Duniya Yana da Shekaru 109

Kaduna: Babban Basarake Ya Yi Bankwana da Duniya Yana da Shekaru 109

  • Majiyoyi sun tabbatar da rasuwar Sarkin Kagarko a jihar Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar, bayan fama da jinya
  • Rahotanni suka ce marigayin ya rasu yana da shekaru 109, lamarin da ya jefa al’ummar Kagarko da masarautar cikin alhini
  • An tabbatar da cewa za a yi sallar jana’izar marigayin gobe Juma’a, 9 ga Janairu 2026, a masallacin masarautar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kagarko, Kaduna - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da rasuwar Sarkin Kagarko da ke jihar Kaduna wanda ya rasu bayan fama da jinya.

An tabbatar da rasuwar marigayin mai suna Alhaji Sa'ad Abubakar wanda ya rasu a yau Alhamis 8 ga watan Janairun 2025.

Sarkin Kagarko ya riga mu gidan gaskiya
Marigayi Sarkin Kagarko, Alh Sa'ad Abubakar yayin wani taro. Hoto: @Better_kaduna.
Source: Twitter

Yaushe za a jana'izar Sarkin Kagarko?

Rahoton Leadership ya tabbatar da cewa marigayin ya bar duniya bayan fama da jinya yana da shekaru 109.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An tabbatar da mutuwar kasurgumin 'dan bindiga a Najeriya

Majiyoyi sun tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izar marigayin a gobe Jama'a, 9 ga Janairun 2026, a masallacin Masarautar Kagarko bayan idar da sallar Juma'a.

Marigayin ya dade yana jagorantar masarautar Kagarko tun a shekarar 2000 wanda ya yi daidai da shekaru 25 kenan.

Kaduna ta yi rashi bayan rasuwar Sarkin Kagarko
Taswirar jihar Kaduna inda Sarkin Kagarko ya rasu. Hoto: Legit.
Source: Original

Sakon ta'aziyyar shugaban karamar hukumar Kagarko

Shugaban Karamar Hukumar Kagarko, Muhuyideen Abdullahi Umar, ya bayyana matuƙar baƙin ciki kan rasuwar Sarkin Kagarko, Alhaji Sa’ad Abubakar a shafin Facebook.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Muhuyideen ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi sarkin, Majalisar Masarautar Kagarko, da al’ummar Karamar Hukumar Kagarko baki ɗaya, inda ya buƙaci jama’a da su yi addu’a tare da nuna haɗin kai a wannan lokaci na alhini.

Alhaji Sa’ad Abubakar na daga cikin sarakunan Kagarko da suka fi daɗewa a kan karagar mulki.

Mulkinsa ya kasance mai cike da zaman lafiya, haƙuri da jajircewa wajen bunƙasa cigaban al’umma.

Ya ce Sarkin ya kasance mutum mai tsananin addini kuma mara nuna bambancin ƙabila, inda ya buɗe ƙofa ga kowa ba tare da la’akari da asalinsa ba, yana ƙarfafa zaman lafiya da mutunta juna a tsakanin al’ummomin da ke cikin karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu zai tsaya takarar gwamnan Neja a 2027? Mohammed Idris ya magantu

Ya ce:

“Dole ne mu gina a kan tubalin haɗin kai da cigaban Kagarko da ya shimfiɗa. Yayin da muke jimamin rashinsa, muna roƙon Allah ya jikansa da rahama, ya kuma ba iyalansa da al’ummarmu juriyar wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.”

Masarautar Zazzau ta yi rashin basarake

A baya, mun ba ku labarin cewa Sarkin Dawakin Tsakar Gida na masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Shehu Idris ya riga mu gidan gaskiya.

Alhaji Ibrahim, ɗan marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya rasu ne yana da shekaru 47 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

A wata sanarwa da masarautar Zazzau ta fitar, ta ce an yi wa marigayi sallar Jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.