Da Gaske Sheikh Pantami zai Auri Aisha Buhari? An Samu Bayanai
- Jita-jita ta karade kafafen sada zumunta cewa tsohuwar Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, na shirin auren Sheikh Isa Ali Pantami
- Rahotannin sun bazu ba tare da wata hujja ko tabbaci daga bangaren Aisha Buhari ko Sheikh Pantami ba, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce
- Sai dai tsohon hadimin marigayi shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya fito fili ya yi karin bayani game da rudanin da aka shiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – A ‘yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta sun cika da rade-radi da ke cewa, tsohuwar Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari za ta auri Sheikh Isa Ali Pantami.
Jita-jitar ta samu karbuwa a tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta, inda ake ta yadawa ba tare da wata sanarwa ta hukuma daga bangarorin da abin ya shafa ba.

Source: Facebook
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bashir Ahmad da ya yi aiki da marigayi Muhammadu Buhari ya kawo karshen jita-jitar.
Yadda jita-jitar auren ta bazu a intanet
Rahotanni sun nuna cewa jita-jitar ta fara yaduwa ne ta hannun wasu shafukan sada zumunta da ke wallafa labarai ba tare da cikakken bincike ba.
Daya daga cikin shafukan, mai suna Adamawa Pulse, ya wallafa wani sako a Facebook da ke nuni da cewa ana zargin Aisha Buhari da Sheikh Isa Ali Pantami na shirin aure.
Sai dai shafin ya amince cewa bayanan da ya wallafa ba su da cikakken tabbaci, yana mai cewa babu wata sanarwa da ta tabbatar da hakan.
Aisha Buhari za ta auri Pantami?
Daya daga cikin hadiman tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi kakkausan martani kan masu yada labarin auren.
Ya bayyana cewa wannan ba zargi ba ne da ya cancanci ya dauki hankali, domin a cewarsa, duk mai hankali zai yi watsi da shi kai tsaye.
Bashir Ahmad ya jaddada cewa labarin da ke cewa Aisha Buhari ta amince za ta auri Sheikh Isa Ali Pantami karya ce tsagwaronta, kuma babu gaskiya a cikinsa.
Babu wata hujja game da auren
Duk da yaduwar labarin, babu wata shaida ko magana daga Aisha Buhari da ke nuna cewa tana da wata alaka ta aure da Sheikh Pantami.
Haka zalika, Sheikh Isa Ali Pantami bai fitar da wata sanarwa ko bayani da ke tabbatar ko nuna amincewa da irin wannan jita-jita ba a shafukansa na sada zumunta.

Source: Facebook
Sheikh Isa Ali Pantami ya taba rike mukamin ministan sadarwa a lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari daga 2019 zuwa 2023.
Aisha Buhari ba za ta sake aure ba
A wani labarin, mun kawo muku cewa Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana cewa ba za ta sake aure ba bayan rasuwar mijinta.
Ta bayyana haka ne a sabon littafin tarihin Buhari da aka rubuta, inda ta fadi wasu abubuwa da dama game da rayuwar marigayin.
Legit Hausa ta rahoto cewa Aisha Buhari ta ce za ta zauna ta cigaba da lura da tarbiyyar 'ya'ya da jikokinta maimakon sake aure.
Asali: Legit.ng

