Tashin Farashi Ya Tunkaro Najeriya bayan Kara Kudin Shigo da Kaya daga Waje

Tashin Farashi Ya Tunkaro Najeriya bayan Kara Kudin Shigo da Kaya daga Waje

  • Rahoto ya nuna cewa kamfanin jigilar kaya na MSC ya sanar da karin kudin shigo da kaya da kudin ajiya a tashoshi daga ranar 1, Janairu, 2026
  • Masana da dillalan shigo da kaya na gargadin cewa karin kudin zai iya kawo tsaiko a fitar da kaya daga tashoshi, tare da karin kudin ajiya
  • Masu shigo da kaya na duba yiwuwar sauya kamfani, yayin da ake kira da a bai wa masu kasuwanci isasshen lokaci kafin irin wadannan canje-canje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Masu amfani da kayayyaki a Najeriya na iya fuskantar karin farashi a kasuwanni bayan kamfanin jigilar kaya mafi girma a duniya, Mediterranean Shipping Company (MSC), ya dauki matakin kara kudin shigo da kaya a cikin gida.

Kara karanta wannan

Nijar da kasashe 2 sun ci bashin wutar lantarkin N25bn a Najeriya sun gaza biya

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da iyalai da dama ke fama da karancin kudi, tare da fargabar cewa karin kudin zai iya dakile saukar hauhawar farashi da aka fara gani a baya-bayan nan.

Wajen da ake sayar da kayan abinci
Kasuwar da ake sayar da kayan abinci. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kara kudin shigo da kaya Najeriya

Business Day ta wallafa cewa bayanan da masu shigo da kaya suka gani sun nuna cewa daga ranar 1, Janairu, 2026, kudin takardun shigo da kaya na kwantena mai tsawon kafa 20 ya tashi daga N45,000 zuwa N58,500.

Kudin shigo da kwantena mai fadin kafa 40 ya karu daga N72,000 zuwa N93,600. Haka kuma, an kara wasu kudin da ake karba a tasha da kashi mai yawa, abin da ke kara nauyi ga ‘yan kasuwa.

Masu ruwa da tsaki a harkar shigo da kaya daga kasashen waje sun bayyana cewa karin kudin ya zo ba tare da isasshen shiri ba.

Sulaiman Ayokunle ya ce yawancin masu shigo da kaya sun riga sun tsara farashin jigila da sayar da kaya bisa tsohon tsarin da aka saba da shi.

A cewarsa, wannan canji na gaggawa na iya jawo jinkirin fitar da kaya daga tashoshi, wanda ke nufin karin kudin ajiya a gare su.

Kara karanta wannan

Ana fargabar yaki bayan Amurka ta tabo Rasha, gwamnatin Putin ta magantu

Ya yi nuni da cewa idan kaya suka dade a tashar jiragen ruwa, kudin da ake biya na karuwa, har ma a wasu lokuta ana iya watsi da kaya ko a yi gwanjonsu.

Ana fargabar tashin farashi a Najeriya

Sulaiman Ayokunle ya jaddada cewa duk wani karin kudi a harkar shigo da kaya daga kasar waje, a karshe masu saye ne ke daukar nauyinsa.

Ya ce idan jimillar kudin shigo da kaya ya karu, ‘yan kasuwa ba su da wata hanya face su yi karin a farashi ga masu saye daga wajensu.

Yadda ake sauke kaya a Legas daga waje
Tashar jirgin ruwa da ake sauke kaya a Legas. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A bayanin da ya yi, ya ce wannan na iya janyo tashin farashin kayan masarufi, musamman abinci da kayayyakin amfani na yau da kullum.

Dalilan karin kudin shigo da kaya Najeriya

A wani taro da MSC ya kira a ranar 29, Disamba, 2025, kamfanin ya bayyana wa masu shigo da kaya da dillalan kaya cewa karin kudin na da nasaba da hauhawar kudin aiki da yanayin tattalin arziki.

Wasu ‘yan kasuwa sun kuma koka da cewa an amince da karin kudin ba tare da tattaunawa kai tsaye da su ba, lamarin da suke ganin ya saba da ka’idojin tuntubar masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

An hango jirgin yakin Amurka ya sauka a Najeriya da dare

Tribune ta rahoto cewa wasu masu shigo da kaya sun bayyana cewa duk da rashin mafita a halin yanzu, suna duba yiwuwar sauya kamfanin jigila nan gaba.

NNPCL ya rage farashin man fetur

A wani labarin, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya rage farashin litar man fetur a wasu sassan birnin tarayya Abuja.

Bayan duba yadda farashin ya ke a wasu gidajen mai a Abuja, Legit Hausa ta gano cewa masu saye za su samu saukin kimamin N20.

Sai dai duka da sauke farashin, kudin litar mai a gidajen mai da ke da alaka da matatar Dangote ya fi araha a kan na kamfanin NNPCL.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng