Babbar Magana: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari 'Wurin Shakatawa' na Gwamnatin Tarayya

Babbar Magana: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari 'Wurin Shakatawa' na Gwamnatin Tarayya

  • 'Yan bindiga sun kai mummunan farmaki gandun dabbobin daji na gwamnatin tarayya a jihar Oyo, sun kashe jami'an tsaron wurin da dama
  • Bayanai sun ce maharan sun bude wa jami'an NPS, masu a'hakin tsare gandun dabbobi a harin da suka kai cikin daren jiya Talata
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da tura jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro da dawo da doka da oda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari wurin da ake killace dabbobin daji wanda ke karkashin gwamnatin tarayya a jihar Oyo.

Maharan sun bude wa jami’an Hukumar Kula da Gandun Dabbobi ta kasa (NPS) a harin, wanda suka kai a ƙauyen Oloka da ke ƙaramar hukumar Orire a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe wani uban daba a Kano da rikici ya barke tsakanin kungiyoyi 2

Jihar Oyo.
Taswirar jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton The Nation ya nuna cewa harin, wanda ya auku a daren Talata, ya yi ajalin mutane da dama, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.

'Yan bindiga sun farmaki jami'an NPS

An ruwaito cewa maharan sun yi mamaya ba tare da tsammani ba, suka afka wurin da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar 6 ga Janairu, 2026, inda suka yi wa jami’an NPS ba-zata.

Rahotannin da suka fito zuwa yanzu, sun nuna cewa jami’ai da dama sun rasa rayukansu, yayin da wasu kuma suka jikkata a yayin harin.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba a hukumance, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da lamarin

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ’yan sandan jihar Oyo, Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Ibadan.

Ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka kwamishinan 'yan sandan jihar Oyo da wasu shugabannin hukumomin tsaro na kan hanyar zuwa wurin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki kauyuka cikin dare, an yi awon gaba da mutane a Katsina

Kakakin 'yan sandan ya ce:

“Eh, haka ne wasu mahara da ba a tantance ko su waye ba kan jami’an National Park. Kwamishinan ’yan sanda tare da sauran shugabannin hukumomin tsaro su na kan hanyarsu ta zuwa wurin da abin ya faru.”

Wane mataki 'yan sanda suka dauka?

A cewarsa, Kwamishinan ’yan sanda, CP Femi Haruna, ya tura dakarun 'yan sanda na musamman, jami'an MOPOL da kuma dakarun sashen EOD zuwa wurin domin dawo da doka ta oda.

Jami'an 'yan sanda.
Jami'an rundunar 'yan sanda a bakin aiki a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ayanlade ya ce:

"CP Femi Haruna ya ba da umarnin tura tawagar jami'ai na musamman, Mobile Police Force (MOPOL) da kuma dakarun sashen EOD zuwa yankin domin hana tabbatar da tsaro da dawo da doka da oda.”

Hukumomin tsaro na ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka kai harin da kuma tabbatar da tsaro a yankin.

Yan bindiga sun sace mutane a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

An hango jirgin yakin Amurka ya sauka a Najeriya da dare

Shaidu sun bayyana cewa hare-haren sun faru ne a daren Litinin, 5 ga watan Janairun 2025 lokacin da ’yan bindigan da ke dauke da manyan makamai suka mamaye yankin.

An tattaro cewa miyagun 'yan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama amma har yanzu babu wata sanarwa a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262