Tsohon Sanata Ya Godewa Tinubu, Wike bayan Jifansa da Shirgegen Mukami

Tsohon Sanata Ya Godewa Tinubu, Wike bayan Jifansa da Shirgegen Mukami

  • Tsohon sanata, Magnus Abe, ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike bayan nadinsa shugaba a majalisar hukumar NUPRC
  • Abe ya ce goyon bayansa ga Tinubu ya ta’allaka ne kan gaskiyar imani da shugabancinsa, ba don neman wani abu ba
  • Ya yi alkawarin ci gaba da biyayya ga Tinubu tare da kira ga ‘yan Najeriya su mara wa ajandar gyaran tattalin arzikin gwamnati baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Sanata Magnus Abe ya mika godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Abe ya yi godiya bayan nadinsa a matsayin shugaban Majalisar da ke sa ido a kan sha'anin Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NUPRC).

Abe ya godewa Wike da Tinubu bayan samun muƙami
Tsohon sanata, Magnus Abe, Bola Tinubu da Nyesom Wike. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abe ya ce goyon bayansa ga Tinubu ba wai don tsammanin lada ba ne, illa saboda cikakken imani da cewa zai tafiyar da mulki ta wata sabuwar hanya, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni bayan 'yan ta'adda sun yi ta'addanci a Neja

Abe ya yi godiya ga Tinubu, Wike

Magnus Abe ya bayyana nadinsa a matsayin babbar dama ta musamman da za ta ba shi damar bayar da gudummawa ga sauyin kasa, musamman a wani muhimmin bangare kamar na man fetur.

A cewarsa:

"Ƙauna ta da goyon bayana ga Shugaba Tinubu sun samo asali ne daga imani cewa zai yi abubuwa daban, kuma Najeriya za ta fi kyau, alƙaluma ma za su nuna hakan.”

Ya kara da cewa manufofin gwamnatin Tinubu sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda alamu ke nuna cewa ƙasar na tafiya kan hanya madaidaiciya.

Ya ce, nadin da Bola Tinubu ya yi masa ya sake nuna kwarewa da dabarun shugabanci da ke sanya shugaban ya zama gogaggen ɗan siyasa.

Sanata Abe ya yaba salon mulkin Tinubu
Tsohon sanata daga jihar Rivers, Magnus Abe. Hoto: Magnus Abe.
Source: Facebook

Abe ya fadi ayyukan alherin Tinubu

Tsohon sanatan ya ce shugabancin Tinubu ya samar da amincewa tsakanin ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da jam’iyya ba.

A cewarsa,:

“Najeriya ba ta zama ƙasa a ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ba, sai dai ‘yan Najeriya sun samu shugaba guda ɗaya da kowa zai iya yarda da shi.”

Kara karanta wannan

Venezuela: An kada hantar Tinubu, an 'gano' shirin Amurka na cire shi a ofis

Ya kuma yi alkawarin ci gaba da biyayya ga Shugaban Ƙasa, yana mai cewa Tinubu uba ne da ke saka wa amintattu da kuma fifita kwarewa.

Abe ya kuma gode wa Nyesom Wike, yana mai cewa gudummawarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen bai wa Tinubu da jam’iyyar APC nasara a Jihar Rivers a zaben 2023, cewar Punch.

A karshe, Magnus Abe ya gode wa Allah tare da kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da masu suka, su biya haraji, su kuma mara wa ajandar gyaran gwamnatin Tinubu baya.

An nemi Wike ya yi murabus daga APC

An ji cewa sakataren jam'iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru ya maida raddi mai zafi ga Ministan Harkokin birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Basiru ya bukaci Wike ya ajiye mukaminsa na minista a gwamnatin APC domin ba zai yiwu su zuba masa ido yana haddasa rikici a jam'iyya ba.

Wannan na zuwa ne bayan Wike ya gargadi Basiru da ya tsame kansa daga harkokin siyasar jihar Rivers.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.