Kwanaki bayan Munanan Hare Hare a Neja, Manoma Sun Ci Karo da Bam a Gona
- Kwanaki kadan bayan munanan hare-hare biyu a jihar Neja, manoma sun gano bam yayin da suka shiga gonakinsu domin yin aiki
- Shugaban Karamar Hukumar Mashegu, Umar Jibril Igade ya tabbatar wa da Legit cewa manoman sun sanar da su, kuma an dauki mataki
- Shugaban Karamar Hukumar Mashegu, Umar Jibril Igade ya kara da cewa tuni aka fara daukan matakan ko ta kwana saboda dakile hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Neja – Wasu manoma a Neja sun yi kicibus da bam yayin da suka shiga gona domin fara aiki, kasa da mako guda bayan wasu munanan hare-hare guda biyu da aka samu a jihar.
Shugaban Karamar Hukumar Mashegu, Umar Jibril Igade, inda lamarin ya faru, ya tabbatar wa Legit faruwar lamarin ta wayar tarho.

Source: Twitter
Haka kuma, fitaccen ɗan jarida a yankin, Kwamred Zakari Y. Adamu Kontogora, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa an tsinci bam ɗin a yankin Zugurma da ke Karamar Hukumar Mashegu.
An gano bam a jihar Neja
A ƙarin bayani da ya yi wa Legit, Shugaban Karamar Hukumar Mashegu, Umar Jibril Igade, ya tabbatar da cewa an fara ɗaukar matakai domin dakile yiwuwar fashewar bam ɗin.
A kalamansa, ya ce:
“Gaskiyar magana, an tsinci bam a wani ƙauye na Zugurma. Manoma suka ga bam ɗin, suka sanar da mu, mu kuma muka sanar da jami’an tsaro. Mun yi gaggawar killace wurin.”
“Da ikon Allah, mun samu nasarar killace wurin nan domin kada a bar jama’a suna kallo abin ya tashi ya jawo asarar rayuka. A halin yanzu, mun killace wurin tun jiya, kuma jami’an tsaro sun ci gaba da tsare wurin.”
Ya ƙara da bayyana cewa tuni aka sanar da jami’an tsaro da suka dace domin su duba al’amarin, da nufin ɗaukar matakan gaggawa da kare rayukan jama’a.

Source: Original
An ɗauki matakan tsaro a Neja
Shugaban karamar hukumar Mashegu a Jihar Neja ya ƙara da cewa an fara taron gaggawa da masu ruwa da tsaki domin ɗaukar matakan kariya.
Ya ce:
“An ƙara faɗaɗa bincike, amma dukkan alamu suna nuna cewa bam ɗin guda ɗaya ne kawai. Mun tura jami’an tsaro tare da ‘yan banga da muke da su, sannan ana ci gaba da duba ko akwai wani irin wannan.”
Ya ƙara da cewa:
“Karamar Hukumar Mashegu a shirye take. Gaskiyar magana, an samu matsaloli a Jihar Neja, kuma sun shafi Karamar Hukumar Mashegu da nake jagoranta, amma muna ɗaukar matakai tun kafin irin wannan ya faru.”
Ya bayyana cewa a halin yanzu ana shirin gudanar da taro da dukkannin jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙara ɗaukar matakan da za su dakile duk wata barazana da ka iya tasowa nan gaba.

Kara karanta wannan
Borno: Sojoji sun taka bama bamai a hanyar kai wa ƴan ta'adda farmaki, an yi asarar rayuka
Matakin da aka dauka bayan harin Neja
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago ya bayyana harin da aka kai Kasuwar Daji da ke yankin Demo a matsayin danyen aiki da rashin imani.
Ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda aka fara sabuwar shekara da irin wannan mummunan labari, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu.
Gwamna Bago ya tabbatar da cewa dakarun tsaro na haɗin gwiwa suna bin sawun ’yan ta’addan domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su su dawo cikin yan uwansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

