An Samu Matsala a Layin Wutar Kano zuwa Katsina, KEDCO Ya ba Mutanen Yankuna 6 Hakuri
- Kamfanin raba wuta na Kano (KEDCO) ya tabbatar da cewa an samu matsalar katsewar layin wuta a wasu sassan jihar Katsina
- KEDCO ya ce lamarin ya faru ne sakamakon gobarar da ta auku a wata taransufoma a tashar wuta da ke IBB Way ranar Lahadi
- Kamfanin ya bai wa mutane hakuri tare da tabbacin cewa tuni kwararrun injiniyoyi suka fara bincike don gano matsalar da kuma gyarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Najeriya - Wasu mazauna jihar Katsina sun fara fuskantar matsalar wutar lantarki bayan gobarar da ta auku wata na'urar rarraba wuta.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), wanda ke da alhakin ba wasu sassan jihar Katsina wuta, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Source: Getty Images
An dauke wuta a wasu sassan Katsina
KEDCO ya bayyana cewa wasu sassan birnin Katsina na fama da katsewar wutar lantarki ne sakamakon gobara da ta shafi na'urar taransufoma a IBB Way, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin KEDCO, Sani Sani, ya fitar a ranar Litinin, kamfanin ya ce lamarin ya faru ne a daren Lahadi.
Bisa haka ne ya bai wa al'ummar unguwannin da matsalar ta shafa hakuri, yana mai tabbatar da cewa tuni kamfanin ya fara kokarin gyara domin dawo masu da hasken wuta.
KEDCO ya gano matsalar da ta auku
Sanarwar ta ce:
“Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) na ba da hakuri ga jama'a a Katsina bisa gobarar da ta shafi na'urar taransufoma mai karfin 15MVA TR3 a tashar da ke IBB Way, a daren Lahadi 4 ga Janairu, 2026.
“Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai a halin yanzu, tawagar kwararrunmu na fannin fasaha suna wajen domin gano dalilin lamarin, tantance girman barnar da ta faru, tare da yin aiki don dawo da wutar lantarki cikin gaggawa.”
Wane mataki kamfanin KEDCO ya dauka?
A matsayin matakin kariya, KEDCO ya ce an cire layin yankunan da lamarin ya shafa domin kare rayuka da dukiyoyi, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarki mai martaba, sun nemi fansar Naira miliyan 450
“Katsewar wutar lantarkin ta shafi wasu sassan birnin Katsina da suka hada da Kofar Kaura, GRA, Dandagoro, wasu sassan Kofar Marusa, Janbango, titin Kano da kewayensu."
“KEDCO na kara ba da hakuri bisa duk wata matsala da hakan ya haifar, tare da tabbatar wa kwastomomi cewa tsaro da dawo da wuta cikin lokaci su ne manyan abubuwan da muka sanya a gaba.”

Source: Original
Kamfanin ya kara da cewa zai ci gaba da fitar da karin bayani kan lamarin yayin da injiniyoyi ke ci gaba da kokarin gyara matsalar domin dawo da hasken wuta.
Wani Bakatsine, Shehu Sani ya shaidawa Legit Hausa cewa rashin wutar lantarkin ya jawo tsaiko ga wasu yan kasuwa, da kuma jefa wasu magidantan cikin karin wahala.
Ya bukaci kamfanin KEDCO da ya yi duk mai yiwuwa wajen gyara wutar lantarkin yankunansu, yana mai cewa suna yabon adadin wutar da ake samu a baya-bayan nan.
"Gaskiya kafin samun wannan matsala muna samun wuta sosai ba kamar baya can ba, dan mutane da dama sun fara dogaro da wuta, amma kwatsam aka daina kawo wa.

Kara karanta wannan
Jerin kungiyoyin 'yan ta'adda 8 da Amurka ta fi damuwa da ayyukansu a Najeriya da Afirka
"To da farko mun shiga damuwa amma da muka ji labarin matsala aka samu, hankalin mu ya dan kwanta, muna fatan a gyara a kan lokaci," in ji shi.
Babban tushen wutar Najeriya ya lalace
A wani labarin, kun ji cewa an samu gagarumar matsalar wutar lantarki a faɗin Najeriya a ranar Litinin biyo bayan durƙushewar babban tushen wutar lantarki na ƙasa.
Kamfanonin rarraba wuta guda takwas ciki har da na Kano da Kaduna ba su samu ko digo na wuta ba sakamakon wannan matsalar.
Wannan rugujewar ta shafi dukkan sassan ƙasar, inda kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) guda uku kacal daga cikin guda 11 suka iya samun wuta daga tushen wutar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
