Shirin 2027: INEC Ta Dawo Rajistar Masu Zabe a Najeriya a Zagaye na 2
- Hukumar INEC ta ce ta dawo da aikin rajistar masu jefa ƙuri’a a faɗin Najeriya bayan kammala zagaye na farko da aka rufe a watan Disamban 2025
- Hukumar ta bayyana cewa miliyoyin ’yan ƙasa sun yi rajistar ta yanar gizo da ta zahiri a zagaye na farko, lamarin da ya nuna sha’awar harkar zaɓe
- Sai dai hukumar INEC ta ce a yanzu an dakatar da rajistar a Anambra da Babban Birnin Tarayya saboda wasu muhimman ayyukan zaɓe da ke gudana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanar da dawo da aikin rajistar masu jefa ƙuri’a a faɗin Najeriya, wanda ke nuna fara zagaye na biyu na shirin.
Dawowar aikin na zuwa ne bayan kammala zagaye na farko da aka rufe a ranar 10, Disamba, 2025, kamar yadda hukumar ta bayyana a baya.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa INEC ta ce ta yi amfani da tazarar da ke tsakanin zagaye na farko da na biyu wajen aiwatar da wasu ayyuka da doka ta tanada, domin tabbatar da sahihancin kundin masu jefa ƙuri’a.
Rajistar da hukumar INEC ta fara a 2025
Hukumar INEC ta fara aikin rajistar masu jefa ƙuri’a ta yanar gizo a ranar 18, Agusta, 2025, kafin daga bisani ta fara rajista ta zahiri a cibiyoyi daban-daban a ranar 25, Agusta, 2025.
A cewar bayanan da hukumar ta fitar, wannan tsari ya bai wa ’yan ƙasa damar fara rajista ta intanet kafin su kammala ta a cibiyoyin da aka tanada a ƙananan hukumomi.
INEC ta bayyana cewa tsarin ya taimaka wajen rage cunkoso da kuma sauƙaƙa aikin ga masu son yin rajista a matsayin masu jefa ƙuri’a.
Adadin masu rajista a zagaye na 1
A wata sanarwa da INEC ta fitar a watan Disamban 2025, hukumar ta ce jimillar ’yan Najeriya 9,891,801 ne suka fara rajista ta yanar gizo a zagaye na farko na aikin.
Daga cikin wannan adadi, INEC ta ce rajistar mutane 2,572,054 ce aka kammala gaba ɗaya zuwa ranar 28, Nuwamba, 2025.

Source: Getty Images
Punch ta rahoto cewa hukumar ta ƙara da cewa rajistar da aka kammala ta haɗa da mutane 1,503,832 da suka kammala rajistarsu ta yanar gizo, sai kuma 1,068,222 da suka yi rajista ta zahiri a cibiyoyin INEC.
Ana rajistar masu zabe zagaye na 2
Yayin sanar da cigaba da rajistar masu zabe a sassan ƙasa, INEC ta ce an dakatar aikin rajista a jihar Anambra da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Hukumar ta danganta dakatarwar da wasu ayyukan INEC da ke gudana a wuraren biyu, wanda ke buƙatar cikakken kulawa da shiri.
Jam'iyyar PDP ta kai INEC kara kotu
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta ce ta shirya kai hukumar zabe kara kotu domin kwato mata hakkinta a jihar Osun.
Shugaban PDP na kasa, Tanimu Turaki ya bayyana cewa an fitar da sunayen 'yan takaran gwamna a Osun ba tare da sanya sunan na su ba.
Tanimu Turaki ya bayyana cewa sun mika dukkan takardu da ake bukata ga INEC, duk da cewa ba su cika fom ta yanar gizon hukumar ba.
Asali: Legit.ng

