Lokaci Ya Yi: An Dawo da Gawar Sanata Najeriya bayan Allah Ya Masa Rasuwa a Indiya
- Gawar sanatan Nasarawa ta Arewa, Godiya Akwashiki ta iso Najeriya daga kasar Indiya bayan Allah ya karbi ransa a asibiti
- Wata majiya daga cikin iyalan marigayin ta bayyana cewa manyan jiga-jigan SDP da abokansa na siyasa ne suka tarbi gawar a Abuja
- Sanata Godiya Akwashiki ya rasu ne a wani asibiti a kasar Indiya ranar Laraba, 31 ga watan Disamba, 2025 bayan fama da jinya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rahotanni sun tabbatar da cewa an dawo da gawar Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Arewa a Majalisar dattawan Najeriya, Godiya Akwashiki.
A makon jiya ne aka tabbatar da rasuwar Sanata Akwashiki a wani asibitin kasar Indiya, inda ya tafi jinyar ciwon da yake damunsa.

Source: Facebook
Wata majiya daga iyalansa, wadda ta yi magana da Premium Times bisa sharadin sakaya sunanta saboda ba ta da izinin hira da kafafen watsa labarai, ta tabbatar da dawo da gawar sanatan Najeriya.
Gawar Sanata Akwashiki ta iso Najeriya
Ta ce an shigo da gawar marigayin ne ta Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya Abuja da safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Janairu, 2025.
Majiyar ta ce abokan siyasar sanatan, shugabannin jam’iyyar SDP da magoya baya ne suka tarbi gawar, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Al-Makura.
Sauran wadanda suka tarbi gawar sun hada da ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo; mukaddashin shugaban SDP na ƙasa, Sadiq Gombe; da kuma wani jigo a Majalisar Wakilai, Gbefwi Gaza.
Sanata Akwashiki, wanda ya kasance mamba a jam’iyyar SDP har ya bar duniya, ya rasu ne a ranar 31 ga Disamba, 2025, yana da shekaru 52.
Takaitaccen tarihin siyasar Akwashiki
Marigayi Akwashiki gogaggen ɗan siyasa ne kuma ƙwararren mai haɗa jama’a tun daga tushe, wanda aka ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan siyasa mafi tasiri a Mazabar Sanatan Nasarawa ta Arewa.
An zaɓe shi a matsayin mamban Majalisar Dattawa ne a ƙarƙashin SDP, lamarin da ya zama babban abin mamaki a siyasar Nasarawa, kasancewar jam’iyyar ba ta da rinjaye a jihar.
Nasarar da ya samu ta sa ya doke manyan jam’iyyun siyasa da suka mamaye siyasar Najeriya, tare da bai wa SDP karin martaba da shahara a matakin ƙasa, in ji Leadership.

Source: Twitter
Kafin zaɓensa zuwa Majalisar Dattawa, Akwashiki ya riƙe muƙamai daban-daban na siyasa a matakin jiha ciki har da mataimakin kakakin Majalisar Nasarawa.
Har zuwa yanzu, iyalansa ba su fitar da cikakken bayani kan tsare-tsaren jana’izarsa ba amma ana tsammanin za su sanar nan ba da jimawa ba.
Tsohon kwamishina ya rasu a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Alhaji Suleiman Lawal Kauru, ya rasu yana da shekaru 78 a asibitin Shika da ke Zaria.
An gudanar da sallar jana'izarsa a Filin Mallawa da ke Tudun Wada, Zaria, inda manyan baki suka halarta, kamar yadda rahoto ya nuna.
Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar har da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, da Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Ya'u Shehu Usman.
Asali: Legit.ng

