Matakin da Gwamnati Ta Ɗauka bayan Ƴan Ta'adda Sun Kashe fiye da Mutum 30 a Neja
- Gwamna Umaru Bago ya yi Allah-wadai da kisan fiye da mutane 30 da yan ta'adda suka yi a kasuwar Borgu dake jihar Niger
- Bago ya tabbatar da cewa dakarun tsaro na haɗin gwiwa suna bin sawun 'yan ta'addan domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su
- Tuni dai Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga shugabannin tsaro na kasa da su kamo wadanda suka aikata kisan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya yi tir da kakkausan harshe game da harin ta’addancin da aka kai wa mazauna ƙaramar hukumar Borgu.
Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan bindiga sun kashe fiye da mutane 30 tare da yin garkuwa da wasu da dama, bayan sun kona kasuwa da rumbunan hatsi.

Source: Twitter
Gwamna ya yi tir da kisan mutane a Neja
Gwamna Bago, ta bakin babban sakataren yaɗa labaransa, Bologi Ibrahim, ya bayyana harin da aka kai Kasuwan Daji da ke yankin Demo a matsayin danyen aiki na rashin imani, in ji rahoton Channels TV.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda aka fara sabuwar shekara da wannan mummunan labari, yayin da ya jajantawa iyalai da al'ummar da abin ya shafa.
Gwamna Bago ya tabbatar da cewa dakarun tsaro na haɗin gwiwa suna bin sawun 'yan ta'addan domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Ya buƙaci jama'a da su dogara ga Allah, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa tana haɗa kai da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin ƙarfafa tsaro a yankunan da ke fuskantar barazana.
'Yan ta'addan, waɗanda ake zargin sun fito ne daga dajin Kainji Lake National Park, sun kai harin ne a ranar Asabar da yamma inda suka yi ta harbin mutane tare da kwashe kayan abinci kafin su cinna wa kasuwar wuta.
Shugaba Tinubu ya ba hafsoshi sabon umarni
Biyo bayan wannan kisan kiyashi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga Ministan Tsaro, shugaban hafsun tsaro, da sauran shugabannin hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata wannan laifi.
Shugaban ya umarci Sufeto Janar na 'yan sanda da shugaban hukumar DSS da su tabbatar an hukunta 'yan ta'addan yadda ya kamata, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Sanarwar da Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta bayyana cewa babban burin gwamnatin shi ne ceto dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su ba tare da ɓata lokaci ba.

Source: Original
An roki gwamnati ta samar da sansanin sojoji
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa 'yan ta'addan sun ɗure kusan mutane 42 suka kashe su ba tare da wani jami'in tsaro ya kawo masu cikas ba, in ji rahoton Punch.
Rundunar 'yan sandan jihar Niger, ta bakin kakakinta Wasiu Abiodun, ta tabbatar da cewa 'yan bindigar sun cinna wa kasuwar wuta tare da sace fasinjoji da dama zuwa daji.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni bayan 'yan ta'adda sun yi ta'addanci a Neja
Wannan hari ya haifar da fargaba a yankin Borgu, inda jama'a ke kira ga gwamnati da ta samar da sansanin jami'an tsaro na dindindin a kusa da dajin National Park domin hana sake aukuwar irin wannan ta'asa.
Mutane 60 aka kashe a kasuwar Neja
A wani labari, mun ruwaito cewa, akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu bayan wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a Kasuwan Daji da ke Borgu a Jihar Neja.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun fito ne daga dajin Kainji, inda suka kewaye kasuwar, suka sace mutane da dama musamman mata da yara, tare da banka wa kasuwa wuta.
Bayan fiye da sa'o'i 12 da harin, ana ci gaba da gano gawarwaki a dazuka da ke kewaye da wajen, yayin da gwamnati ta bayyana matakan da take ɗauka domin dakile hare-hare.
Asali: Legit.ng

