Kamfanin NNPCL Ya Sanar da Sauke Farashin Litar Man Fetur

Kamfanin NNPCL Ya Sanar da Sauke Farashin Litar Man Fetur

  • Kamfanin NNPCL ya sanar da sake rage farashin litar man fetur da N20 a gidajen mansa, matakin da zai shafi masu saye da sayarwa
  • Sabon farashin ya fara bayyana ne a wasu manyan gidajen mai a Abuja, inda aka ce matakin ya biyo bayan umarnin da aka ba kamfanin
  • Duk da wannan ragin da aka samu, farashin NNPCL har yanzu ya fi na wasu gidajen mai da ke samun kaya daga matatar Dangote

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya sake rage farashin man fetur da N20 a gidajen mai da ke karkashinsa, sauyin ya zo ne a wani sabon yunƙuri na daidaita farashi.

Binciken da aka gudanar a wasu gidajen mai na NNPC a birnin tarayya Abuja ya nuna cewa yanzu ana sayar da litar man fetur a kan N815, maimakon N835 da ake sayarwa a baya.

Kara karanta wannan

Mamdani: Musulmin da ya ci zabe ya ruguza shirin Isra'ila a Amurka

Mutane suna sayen fetur a gidajen mai
Masu sayen fetur a wani gidan mai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tribune ta wallafa cewa majiyoyi daga cikin kamfanin sun bayyana cewa sauke farashin ya biyo bayan wani umarni na cikin gida da aka amince da shi a daren Lahadi, 4 ga Janairun 2026.

Inda aka fara ganin sabon farashin mai

Rahotanni sun nuna cewa sabon farashin N815 kan kowace lita ya fara bayyana a gidajen mai na NNPC da ke Wuse Zone 4 da Zone 6, da ke kan hanyar Keffi–Abuja, da kuma wasu gidajen mai da ke kan Kubwa Expressway.

Masu saye sun tabbatar da cewa sauyin farashin ya zo musu a matsayin rangwame, duk da cewa har yanzu suna kwatanta shi da farashin da ake samu a wasu gidajen mai masu zaman kansu.

Sai dai duk da wannan ragi, farashin man fetur a gidajen mai na NNPC ya kasance ya fi na wasu gidajen mai da ke sayar da lita a N739, wanda hakan ke nuna tazara mai yawa a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa dajin Sambisa, sun yi kaca kaca da Boko Haram

Bambancin farashin man fetur a Najeriya

Gidajen mai na MRS, waɗanda ke samun man fetur daga matatar Dangote, na sayar da litar mai a farashin N739 a faɗin ƙasa. Wannan ya sanya farashin NNPC ya kasance ya fi na su da N79.

Rahotanni sun nuna cewa matatar Dangote ta taka rawa wajen sauya yanayin kasuwar man fetur a ’yan makonnin nan, inda rage farashin da ta yi ya jawo gasa mai tsanani tsakanin ’yan kasuwa.

Wasu masu sayen mai a gidan mai
Yadda ake sayar da fetur a gidan mai. Hoto: Imran Muhammad
Source: Twitter

Wannan gasa ta sa kamfanoni da dama ke sake duba farashinsu domin jawo hankalin masu saye, musamman a manyan birane da ake yawan saye da sayarwa.

NNPC ya rage farashin man fetur

A wani labarin, kun ji cewa NNPCL ya rage farashin man fetur da N80 a ranar 19, Disamba, 2025, inda farashin ya sauka zuwa N835 kan kowace lita a wancan lokacin.

Ragin da aka yi a wancan lokaci ya biyo bayan tsananin gasa da ta ɓarke a kasuwar man fetur, bayan matatar Dangote ta rage farashin mai zuwa N699 kan kowace lita.

Ana ganin cewa ci gaba da wannan gasa na iya sa a samu ƙarin sauye-sauye a farashin man fetur a nan gaba, yayin da kamfanoni ke ƙoƙarin daidaita ribarsu da kuma jan hankalin masu saye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng