Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Mutum 60 a Kasuwar Neja ana Hada Hada
- Akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu bayan wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a Kasuwan Daji da ke Borgu a Jihar Nijar, inda aka kashe ’yan kasuwa da masu sayayya
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun fito ne daga dajin Kainji, inda suka kewaye kasuwar, suka sace mutane da dama musamman mata da yara, tare da banka wa kasuwa wuta
- Bayan fiye da sa'o'i 12 da harin, ana ci gaba da gano gawarwaki a dazuka da ke kewaye da wajen, yayin da gwamnati ta bayyana matakan da take ɗauka domin dakile irin waɗannan hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja - Akalla mutane 60 ne aka tabbatar sun mutu bayan wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a Kasuwan Daji da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja.
Majiyoyi sun ce ’yan bindigar sun fito ne daga dajin Kainji, inda suka isa kasuwar da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, suka kewaye ta gaba ɗaya kafin su fara kashe ’yan kasuwa da masu sayayya ba tare da tausayi ba.

Source: Twitter
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa bayan harin kasuwar, maharan sun bazu cikin al’ummar yankin, inda suka ci gaba da kashe mutane, sace wasu, tare da lalata dukiyoyi a wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da yankin.
Yadda aka kai harin a Kasuwar Daji
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ’yan bindigar na shiga kasuwar, suka tara mutane da dama, musamman ’yan kasuwa, inda suka ɗaure wasu daga cikinsu kafin su kashe su.
An ce aƙalla ’yan kasuwa 30 aka ɗaure aka kashe su a wuri guda.
Bayan haka, maharan sun fara sace mutane da dama, ciki har da mata da yara. Daga cikin waɗanda aka sace akwai ɗalibai da yara ’yan makarantar St. Mary’s da ke Papiri, waɗanda gwamnatin tarayya ta ceto su kwanan nan.
Vanguard ta rahoto cewa harin bai tsaya a kasuwar ba, domin ’yan bindigar sun kwashe kayan abinci da dukiyoyi masu darajar miliyoyin Naira kafin su banka wa kasuwar wuta.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni bayan 'yan ta'adda sun yi ta'addanci a Neja
'Yan bindiga sun kashe mutum 60 a Neja
Rahotanni daga yankin sun ce fiye da sa'o'i 12 bayan harin, mutanen ƙauyukan makwabta na ci gaba da gano gawarwaki a cikin dazuka da ke kewaye da yankin.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an birne gawarwaki 43, ciki har da Musulmi da Kiristoci a rana guda ranar Lahadi, yayin da ake ci gaba da bincike da gano wasu.
Wasu mazauna yankin sun ce adadin waɗanda suka mutu na iya haura 60, domin akwai waɗanda suka tsira da raunukan harbi.
Wani mazaunin yankin, Marcus Philips Adoka, ya ce sun ga hayaƙi mai yawa daga kasuwar da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, yana mai cewa an tara mutane aka kashe su “kamar awaki da kaji,”

Source: Twitter
Kwamishinan yaɗa labaran Jihar Neja, Obed Nuhu Nana, ya bayyana cewa maharan sun kai hari wani ofishin ’yan sanda a Shafacci da wata makarantar Katolika a Sukumbara kuma ana cigaba da daukar mataki.
Sojoji sun kashe Boko Haram a Sambisa
A wani labarin, mun kawo muku cewa sojojin Najeriya sun kai wani gagarumin farmaki maboyar Boko Haram a dajin Sambisa a Borno.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun Najeriya sun yi musayar wuta da 'yan Boko Haram kafin sojoji su yi nasarar kashe wasu daga cikinsu.
Bayan kashe wasu 'yan ta'addan Boko Haram, sojojin Najeriya sun kwato makaman da mayakan ke amfani da su wajen kai hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

