Wata Mata Ta Yi Tsirara a Dakin Babban Fasto a Otel, Ta ba Shi Mamaki

Wata Mata Ta Yi Tsirara a Dakin Babban Fasto a Otel, Ta ba Shi Mamaki

  • Fasto Enoch Adeboye ya ba da labarin wani abu da ya ce ya faru da shi a yayin wani taron RCCG, inda ya jaddada tasirin addu’a wajen kawo sauyi ga rayuwar mutum
  • Ya ce wata mata ta matsa masa ya bi ta zuwa ɗaki a otel duk da ƙin amincewarsa da farko, abin da daga baya ya haifar da abin mamaki bayan ta fadi dalilin hakan
  • Faston ya bayyana abin da ya gani bayan ta tube kayanta a gabansa da kuma yadda addu’a ta sauya yanayin cikin kankanin lokaci, yana mai cewa darasi ne babba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Babban Faston cocin RCCG, Enoch Adeboye, ya bayyana wani abin mamaki da ya ce ya faru da shi a wata tafiya, inda ya shaida warkewar wata mata bayan addu’a da ya mata.

Kara karanta wannan

Da gaske Amurka ta yi shirin kashe Sheikh Gumi? Malamin ya magantu

Faston ya ruwaito labarin ne a yayin babban taron shekara-shekara na cocin RCCG, yana mai cewa abin da ya faru ya ƙara masa tabbaci kan ikon Allah da kuma ƙarfin addu’a.

Fasto Enoch Adeboye
Fasto Enoch Adeboye yana wani jawabi. Hoto: @rccghq
Source: Twitter

Tribune ta rahoto Enoch Adeboye ya ce lamarin ya faru ne a wani birni da ya ziyarta, inda ya sauka a wani otel ba tare da bayyana sunan garin ba.

Yadda matar ta tunkari Fasto Adeboye

Fasto Adeboye ya ce matar ta same shi ne bayan ya isa otel ɗin da ya sauka, inda ta gaishe shi tare da nuna sha’awar a yi mata addu’a. Ya ce tun farko ya yi ƙoƙarin yi mata addu’a a wurin da suka haɗu, ba tare da buƙatar zuwa ɗakin otel ba.

A cewarsa, ya roƙe ta da kada ta jefa shi cikin matsala, yana mai cewa zai iya yi mata addu’a nan take. Sai dai duk da wannan roƙo, matar ta nace cewa sai ta bi shi zuwa ɗakin da ya sauka.

A wani bidiyo da wani mai amfani da X ya wallafa, Faston ya bayyana cewa wannan nacewa ta sa ya yi mamaki, amma daga ƙarshe ya amince ne domin jin dalilin da ya sa matar ke matsa masa lamba.

Kara karanta wannan

'Shugaba Bola Tinubu zai sanya wa Najeriya sabon suna'

Mata ta yi tsirara a gaban Fasto Adeboye

Suna isa ɗakin, Fasto Adeboye ya ce matar ta bayyana masa dalilin da ya sa ta nace sai ta same shi a keɓe. Ya ce a nan ne matar ta tube kayanta domin nuna masa halin da jikinta yake ciki.

Faston ya ce abin da ya gani ya ba shi mamaki ƙwarai, inda ya bayyana cewa jikin matar cike yake da tabo da raunuka masu yawa.

A cewarsa, ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya fara yi mata addu’a, yana mai cewa bai damu da hayaniya ko wajen da suke ba a otel din, domin abin da ya fi muhimmanci shi ne neman taimakon Allah.

Fasto Enoch Adeboye
Shugaban cocin RCCG, Enoch Adeboye. Hoto: @rccghq
Source: Facebook

Fasto Adeboye ya ce yayin da yake ci gaba da addu’a, sai ya lura da wani sauyi mai ban mamaki a jikin matar. Ya bayyana cewa kafin ya ankara, duk tabon da ya gani a jikinta sun ɓace.

Malaman addini sun yi taro a Legas

Kara karanta wannan

Bam a masallaci: Wanda ake zargi ya fadi makudan kudi da aka ba shi a Borno

A wani labarin, kun ji cewa wasu malaman addinin Musulunci daga fadin duniya sun yi gagarumin taro a birnin Legas na Najeriya.

An ce malamai sun hadu daga kasashe kamar Amurka, Saudiyya, Canada da wasu yankunan nahiyar Afrika a wajen taron da aka yi.

Daya daga cikin shugabannin da suka shirya taron ya bayyana cewa sun hadu ne domin neman mafita kan abubuwan da suka shafi Musulmi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng