Gwamnonin Arewa Sun Yi Magana da Murya Daya kan Harin da Aka Kai Kasuwar Neja

Gwamnonin Arewa Sun Yi Magana da Murya Daya kan Harin da Aka Kai Kasuwar Neja

  • Kungiyar Gwamnonin Arewa ta yi Allah-wadai da kisan yan kasuwa 30 da yan ta'adda suka yi a kasuwar jihar Niger a yau
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci jami'an tsaro su kamo bata-garin da suka kona kasuwar tare da yin garkuwa da mata masu yawa
  • Gwamnonin sun kuma mika ta'aziyya ga jihar Yobe kan hatsarin jirgin ruwa da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) a ranar Lahadi ta nuna bacin ranta tare da yin tir da kakkausan harshe game da harin ta’addancin da aka kai Kasuwan Daji da ke yankin Borgu a jihar Niger.

Rahotanni sun nuna cewa akalla yan kasuwa 30, ciki har da mata, maharan suka kashe, sannan suka yi garkuwa da wasu da dama tare da kona kasuwar baki daya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a kasuwa, an rasa rayukan mutane da dama a Neja

Gwamnonin Arewa sun yi Allah wadai da harin kasuwa a Neja
Kungiyar gwamnonin Arewa suna gudanar da taro. Hoto: @GovernorInuwa
Source: Twitter

Gwamnonin Arewa sun magantu kan harin Neja

Gwamnonin sun bayyana wannan hari a matsayin cin mutunci ga rayuwar talakawa da kuma barazana ga zaman lafiya, in ji rahoton jaridar Punch.

Shugaban kungiyar, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ta bakin daraktan yada labaransa, Ismaila Misilli, ya bayyana cewa wannan danyen aiki ya haifar da bakin ciki ga iyalai da dama tare da dagula harkokin tattalin arziki a yankin.

Yahaya ya jaddada cewa kai hari ga mata da yan kasuwa abin kyama ne da ya saba wa dukkan koyarwar addini da na dan Adam.

Shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan kisa domin su fuskanci shari'a.

Gwamnonin sun magantu kan hadarin jirgin ruwa

Baya ga maganar tsaro, kungiyar gwamnonin arewar ta kuma mika sakon ta’aziyyarta ga gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan hadarin jirgin ruwan da ya faru a Nguru.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarki mai martaba, sun nemi fansar Naira miliyan 450

Hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 25, yayin da wasu 14 har yanzu ba a san inda suke ba bayan jirgin ya kife a kogin Yobe, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa wannan babban rashi ne da ke nuna bukatar gaggawa ta inganta tsaron hanyoyin sufurin ruwa a yankin.

Albashir din gwamnoni ga 'yan Arewa

Kungiyar ta bukaci mahukunta da su kara kaimi wajen gudanar da aikin ceto ga wadanda suka bace, sannan su tabbatar wadanda suka tsira sun samu kulawar da ta dace.

Gwamnonin sun tabbatar wa yan Arewa kudirinsu na ci gaba da hada kai da gwamnatin tarayya domin samar da ingantaccen tsaro da kuma agajin gaggawa ga yankunan da bala’i ya shafa.

Sun kuma yi kira ga jama'a da su kasance masu hadin kai da juriya a wannan mawuyacin lokaci, kamar yadda wasikar ta nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com