Mummunar Gobara Ta Tashi a Ofishin Ƴan Sanda, Ɗakin Ajiye Makamai Ya Ci Wuta

Mummunar Gobara Ta Tashi a Ofishin Ƴan Sanda, Ɗakin Ajiye Makamai Ya Ci Wuta

  • Gobara ta cinye ofisoshi da taskar makamai na rundunar yan sandan Mopol 13 a Makurdi dake jihar Benue a safiyar ranar Lahadi
  • Ganau ya bayyana cewa wutar ta fara ne daga ofishin kwamandan rundunar kafin ta bazu zuwa sauran sassan ginin ta lalata makamai
  • Kakakin yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar gobarar inda tace ana gudanar da bincike domin sanin abin da ya haddasa wutar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da aukuwar wata mummunar gobara wadda ta lashe babban ginin rundunar ‘yan sandan Mopol 13 da ke birnin Makurdi.

Wannan lamari, wanda ya faru a safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Janairu, 2026, ya haifar da gagarumar asara, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga: Sojoji sun yi ruwan bama bamai a Kano, an kashe miyagu 23

Rundunar 'yan sanda ta yi asarar makamai bayan gobara ta babbake dakin ajiyar makamanta
Shugaban rundunar 'yan sanda, Kayode Egbetokun yana magana da manema labarai. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Gobara ta tashi a ofishin 'yan sanda

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa wutar ta kone ofisoshin gudanarwa da kuma muhimmiyar taskar ajiye makamai ta rundunar 'yan sandan Mopol din baki ɗaya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Udeme Edet, ta tabbatar wa manema labarai faruwar wannan lamari, kodayake ta bayyana cewa rundunar tana kan matakin tattara cikakkun bayanai kafin ta fitar da sanarwa.

"Haka ne, na sami labarin gobarar da ta tashi a ginin Mopol 13 da ke Makurdi, amma zan dawo gare ku da cikakken bayani nan gaba," in ji Udeme Edet yayin tattaunawa da manema labarai.

A cewar wasu shaidun gani da ido, gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe. Wani jami'i da yake bakin aiki a lokacin ya bayyana cewa ya ga hayaƙi yana tashi daga ofishin babban kwamandan rundunar.

Wuta ta kone dakin ajiyar makamai

Kafin a farga, hayaƙin ya rikide zuwa babban harshen wuta wanda ya mamaye dukkan ginin, a cewar rahoton Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a kasuwa, an rasa rayukan mutane da dama a Neja

Jami'in ya ƙara da cewa:

"Na kira shugabana cikin gaggawa, wanda shi kuma ya tuntuɓi hukumar kashe gobara. Sai dai kafin isowar jami'an kwana-kwana, wutar ta riga ta mamaye ko'ina, har ta kai ga kone dukkan kayayyakin da ke ciki."

Wasu faifan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna girman barnar, inda aka ji muryar wani mutum cikin raɗadi yana bayyana cewa dukkan makaman da ke cikin taskar sun zama toka.

An fara bincike don gano musabbabin tashin gobara a ofishin 'yan sandan Benue
Taswirar jihar Benue da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An fara bincike kan musabbabin gobara

Wannan ya tayar da fargaba game da asarar muhimman makamai da kayayyakin tsaro na rundunar waɗanda ake amfani da su wajen yaƙi da miyagun ayyuka a jihar.

Har zuwa yanzu, ba a tantance ko wutar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki ko kuma wani dalili na daban ba.

Rundunar ‘yan sandan ta keɓe yankin domin gudanar da bincike na kwararru don tantance girman asarar da aka yi.

Wannan gobara babban rashi ne ga sashen tsaron jihar Benue, musamman ganin muhimmancin rundunar Mopol 13 wajen wanzar da zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikici.

Kara karanta wannan

Abun ya yi muni: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari Kebbi, an rasa rayuka

Wuta ta babbake ofishin 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata gobara da ta taso daga wata tankar mai ta kone wani sashe na ofishin ‘yan sanda da ke Okokomaiko a jihar Legas.

Rahotanni sun ce tankar ta kama da wuta ne a lokacin da take zuba man dizal a cikin tankin ajiyar wani otel da ke da katanga daya da ofishin jami’an ‘yan sanda.

Lamarin dai ya haifar da turereniya da rige-rige yayin da dukkan ma’aikatan otal din da ‘yan sandan da ke aiki a caji ofis suka tsero daga ofishinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com