Shugaba Tinubu Ya ba Jami'an Tsaro Umarni bayan 'Yan Ta'adda Sun Yi Ta'addanci a Neja
- 'Yan ta'adda sun kashe bayin Allah tare da yin awon gaba da mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Neja
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi Allah wadai da mummunan harin wanda aka kai a wata kasuwa
- Mai girma Bola Tinubu ya yi wa mutanen jihar Neja ta'aziyya tare da umartar jami'an tsaro su gaggauta ceto wadanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga sojoji, ‘yan sanda da hukumar tsaro ta DSS da su farauto tare da cafke wadanda suka kai harin Kasuwan Daji a jihar Neja.
Hakan na zuwa ne bayan ‘yan ta’adda sun kashe akalla mutane 30, tare da sace mata da kananan yara da dama.

Source: Facebook
Umarnin Shugaba Tinubu na kunshe ne a cikin sanarwar da hadiminsa, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamban 2026.
Wane umarni Shugaba Tinubu ya ba da?
Shugaban kasar ya umarci hukumomin tsaro da su ceto duk wadanda aka sace cikin gaggawa, yana mai gargadin cewa ‘yan ta’addan dole ne su fuskanci cikakken hukunci kan ayyukansu na ta’addanci.
Tinubu ya alakanta harin da aka kai a ranar Asabar da ‘yan ta’addan da ke tserewa daga jihohin Sokoto da Zamfara, biyo bayan harin sama da Amurka ta kai musu a daren Kirsimeti.
‘Yan bindiga sun kashe mutane 30, ciki har da mata, a yayin harin da suka kai kasuwar Kasuwan Daji da ke kauyen Demo, karamar hukumar Borgu ta jihar Neja, a ranar Asabar, 3 ga Janairu, 2026. Maharan sun kuma sace mutane da dama, tare da kone kasuwar baki daya.
“Wadannan ‘yan ta’adda sun kure hakurin kasarmu da al’ummarta. Don haka dole ne su fuskanci cikakken sakamakon ayyukansu na laifi. Ko su waye, ko menene manufarsu, dole ne a farauto su.”
“Su da duk wanda ya taimaka musu ko ya basu kariya ta kowace hanya, za a cafke su kuma a gurfanar da su gaban shari’a."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyya
Shugaban kasar ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu, da kuma gwamnati da al’ummar jihar Neja, yana mai tabbatar da cewa an riga an umarci hukumomin tsaro da su kara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke cikin hadari.
Shugaba Tinubu ya bayar da wadannan umarnin ne a matsayin martani ga kisan gillar da aka yi wa mutanen kauyuka a jihar Neja, wanda ake zargin ‘yan ta’addan da suka tsere daga Sokoto da Zamfara bayan harin saman Amurka ne suka aikata.
Shugaban kasar ya yi kakkausar suka ga harin da aka kai al’ummar Kasuwan Daji, tare da yin Allah-wadai da sace mata da kananan yara.
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kano

Kara karanta wannan
Jerin kungiyoyin 'yan ta'adda 8 da Amurka ta fi damuwa da ayyukansu a Najeriya da Afirka
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar ragargazar 'yan bindiga a jihar Kano.
Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga 23 bayan sun farmake su a kananan hukumomin Shanono da Tsanyawa.
'Yan bindigan sun gamu da ajalinsu ne lokacin da suke dawowa daga wajen jana'izar 'yan uwansu da jami'an tsaro suka kashe.
Asali: Legit.ng

