Dalla-dalla: Rukunin Mutane 7 da Ya Zama Dole Su Biya Haraji a Najeriya

Dalla-dalla: Rukunin Mutane 7 da Ya Zama Dole Su Biya Haraji a Najeriya

  • Sabon tsarin haraji na Najeriya ya fara aiki a watan Janairun 2026, inda ya fayyace a sarari wajibcin biyan haraji ga ‘yan kasa da kuma ‘yan kasuwa
  • Ana bayyana sauye-sauyen a matsayin mafi girman garambawul da aka taba yi wa tsarin harajin Najeriya tun bayan samun ‘yancin kai
  • Legit.ng ta fayyace muhimman rukunin mutanen da doka ta tanadar su biya haraji, da kuma wadanda aka ware daga biyan haraji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gwamnatin Najeriya ta fara aiwatar da sabuwar dokar haraji a ranar 1 ga Janairu, 2026, a matsayin wani bangare na yunkurin kara samun kudaden shiga.

Gwamnatin tarayya ta ce dokar ta bayar da karin haske kan wadanda doka ta wajabta su biya haraji da yadda wajibcin ke shafar daidaikun mutane, ‘yan kasuwa da masu kadarori.

Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kudi da gyaran haraji, ya ce sauye-sauyen na da nufin kawar da kuskuren fahimta da ya yadu cewa haraji ya shafi manyan kamfanoni ko attajiran Najeriya ne kawai.

Kara karanta wannan

An fitar da tambarin sabuwar hukumar haraji ta Najeriya bayan Tinubu ya rusa FIRS

Ya bayyana cewa a karkashin tsarin haraji na Najeriya, ana dora wajibci ne bisa samun kudin shiga da riba, ba wai matsayin mutum a al’umma ko girman kasuwancinsa ba.

Gwamnatin Najeriya za ta karbi daga mutum 7 a matsayin haraji
Yadda tsarin haraji zai shafi wasu mutane | Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Hukumomi sun ce fahimtar wadanda doka ta shafa na da matukar muhimmanci wajen kara bin doka da rage keta doka;

Rukunin mutanen da ake sa ran su biya haraji a Najeriya

Ga jerin mutanen da doka ta tanada su biya haraji a Najeriya:

Masu albashi (ma’aikata)

Mutanen da ke samun kudin shiga na dindindin daga aiki a bangaren gwamnati ko masu zaman kansu dole ne su biya harajin kudin shiga na mutum, yawanci ta tsarin Pay As You Earn (PAYE).

Misalai sun hada da ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, ma’aikatan gwamnati na tarayya da jihohi, ma’aikatan kwangila da ke kan albashi, da masu karbar albashi na wata-wata ko mako-mako.

Masu zaman kansu da ‘yan kwangila (freelancers)

Mutanen da ke samun kudin shiga ta kansu su ma dole ne su biya haraji, kuma su ne ke da alhakin mika bayanan harajinsu ga Hukumar Haraji ta jiharsu.

Misalai sun hada da masu sana’o’in hannu, ‘yan kasuwa, kwararru da masu ba da shawara, masu aiki ta intanet, ‘yan POS, direbobin tasi ko na manhajojin sufuri, masu daukar hoto, masu sayar da abinci, masu gyaran gashi da kafintoci.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan bukatar neman hana aiwatar da sababbin dokokin haraji

Kamfanoni da kasuwanci masu rijista

Kamfanonin da aka yi wa rijista a Najeriya doka ta wajabta musu su gabatar da bayanan haraji na shekara-shekara tare da biyan harajin ribar kamfani.

Misalai sun hada da kamfanonin mallaka na iyaka, hadin gwiwar kasuwanci, kamfanoni masu tasowa, masana’antu, otel-otel, kamfanonin safuri, ‘yan kasuwa da kamfanonin ba da shawara.

Kamfanonin kasashen waje da ke samun kudi a Najeriya

Kamfanonin da ba na Najeriya ba amma ke aiki a kasar ko ke samun kudin shiga daga Najeriya dole ne su biya haraji kan ribar da ta shafi wadannan ayyuka.

Misalai sun hada da kamfanonin jigilar kaya na kasashen waje, dandamalin yanar gizo da ke cajin ‘yan Najeriya, kamfanonin hidimar mai da kamfanonin shawara na kasashen waje da ke gudanar da ayyuka a Najeriya.

Masu kadarori da ke samun ribar sayarwa

Mutanen da ke samun riba daga sayar da kadarori dole ne su biya harajin ribar kadarori (capital gains tax) kan ribar da suka samu.

Kara karanta wannan

Dokar haraji: Gaskiyar zance kan batun cire kudi daga asusun banki

Misalai sun hada da sayar da fili, gida ko kadarorin gona, hannun jari, kadarorin zuba jari da injinan kasuwanci da aka sayar da riba.

Kamfanonin mai da makamashi

Kamfanonin man fetur da iskar gas da ke aikin hakar mai suna biyan haraji bisa ka’idoji na musamman, ciki har da harajin ribar man fetur; gwargwadon girma da yanayin bangaren.

‘Yan Najeriya da ke aiki wa kamfanonin kasashen waje

‘Yan Najeriya da ke zaune a kasar amma suna samun kudin shiga daga kasashen waje, ciki har da masu aiki daga gida (remote work), dole ne su biya haraji a Najeriya bisa zama da tushen kudin shiga.

Waɗanda ba a wajabta musu biyan haraji ba

  1. Yara da ba su da kudin shiga
  2. Mutanen da ba sa samun kudin shiga ko riba
  3. Marasa aikin yi da ba su da wata hanyar kudin shiga
  4. Kananan yara, face suna gudanar da kasuwanci bisa doka

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng