Venezuela: An Kada Hantar Tinubu, an ‘Gano’ Shirin Amurka na Cire Shi a Ofis

Venezuela: An Kada Hantar Tinubu, an ‘Gano’ Shirin Amurka na Cire Shi a Ofis

  • Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu game da rashin tsaro da kuma manakisar kasar Amurka a Najeriya
  • Ayodele ya bayyana cewa shugaban Amurka, Donald Trump, na shirin ganin an cire Bola Tinubu daga mulki
  • Limamin ya ce tallafin tsaro da Amurka ke bai wa Najeriya ba wai don kawo karshen rashin tsaro ba ne, illa wata dabara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya gargadi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Fasto Ayodele ya bayyana cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, na da shirin ganin an cire shi daga kujerar shugabancin Najeriya.

Malami ya zargi Trump da shirin cire Tinubu a mulki
Shugaba Donald Trump da Fasto Elijah Ayodele. Hoto: Donald J Trump, Primate Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Trump: Fasto ya gargadi Tinubu

Hakan na cikin wata sanarwa da mataimakin sa na yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar a ranar Lahadi 4 ga watan Janairun 2026, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawo shirin tallafi na 2026, talakawa miliyan 10 za su amfana

Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ya taka rawa wajen kifar da Shugaban Kasar Venezuela, Nicolás Maduro, lamarin da ya janyo fargaba a wasu kasashe.

Fasto Ayodele ya ce Trump ya gama da Tinubu, kuma burinsa na karshe shi ne ganin shugaban Najeriyar ya rasa mukaminsa.

Ayodele ya bayyana cewa taimakon da Amurka ke bai wa Najeriya wajen yaki da rashin tsaro ba kyauta ba ne, illa wata hanya ta shiga cikin tsarin mulki da harkokin siyasar kasar.

Ya ce:

“Trump ya kuduri aniyar cire Shugaba Tinubu. Amurka za ta kasance cikin wadanda za su yi adawa da Tinubu. Ko da ba ku ganin abin kamar yadda ake nuna mini ba, gaskiyar magana ita ce Trump na son a cire Tinubu daga mulki.”

Limamin ya kara da cewa, ko Najeriya ta samu nasara wajen yaki da rashin tsaro ko a’a, Trump bai mayar da hankali kan kawo karshen matsalar tsaro ba, sai dai kawai cimma manufarsa ta siyasa.

A cewarsa:

“Najeriya za ta ci gaba da yaki da rashin tsaro, amma Trump ya riga ya mayar da hankali kan cire Tinubu daga ofis, ko Tinubu ya sani ko bai sani ba. Ba batun tsaro yake ba, ya san abin da yake so.”

Kara karanta wannan

'Tinubu ya cikawa kabilar Ibo burinsu na son kafa kasar Biyafara,' Umahi

Fasto ya gargadi Tinubu kan manakisar Amurka
Fasto Elijah Ayodele da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Primate Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Shawara Ayodele ga Bola Tinubu

Ayodele ya shawarci Shugaba Tinubu da ya dauki matakin siyasa mai karfi da gaggawa domin dakile shirin Trump, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan zai kai ga faduwarsa.

Ya ce Tinubu bai kamata ya sassauta kokarinsa ba, sai ya bullo da sababbin dabaru domin kare kansa da gwamnatinsa, in ba haka ba, zai kare da shan kaye yayin da makiyansa ke murnar faduwarsa.

Wannan furuci na Ayodele ya kara jawo muhawara a siyasar Najeriya, musamman game da rawar da manyan kasashen duniya ke takawa a harkokin cikin gida na kasashen Afirka, cewar Daily Post.

Ayodele ya shawarci Tinubu kan tsaro

An ji cewa ana ci gaba da muhawara kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita Najeriya.

Primate Elijah Babatunde Ayodele ya sanar da Bola Tinubu abin da zai kawo karshen matsalar wadda aka dade ana fama da ita.

Malamin addinin Kiristan ya kuma ba Shugaba Tinubu shawara kan matakan da ya kamata ya dauka don murkushe barazanar 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.