An Shiga Jimami: Malami Ya Fadi Matacce Yayin Murnar Shiga Sabuwar Shekara
- Al'ummar Kiristoci sun shiga wani irin yanayi bayan sanar da mutuwar daya daga cikin manyan Fastoci yayin murnar sabuwar shekara
- Cocin Katolika ya tabbatar da rasuwar Limami Rabaran Stephen Chukwuma, wanda ya rasu a daren sabuwar shekara
- Za a gudanar da jana’iza a ranar 28 ga Janairu, 2026 a Cocin St. Paul’s Cathedral, Issele-Uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Cocin Katolika na Issele-Uku a Jihar Delta ya tabbatar da rasuwar Rabaran Dr. Stephen Chukwuma.
Marigayin kafin rasuwarsa shi ne Limamin Cocin St. John the Baptist Catholic Church, Boji-Boji Agbor, a Karamar Hukumar Ika ta Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
Babban Fasto ya rasu a Delta
Rahoton Vanguard ya nuna cewa limamin ya rasu ne a daren Sabuwar Shekara, bayan ya fadi a yayin da yake gabatar da huduba a coci.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC
A wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na cocin, Rabaran Dr. Charles Uganwa, ya sanya wa hannu, cocin ta bayyana cewa Fr. Chukwuma ya rasu a ranar Laraba, 31 ga Disamba, 2025.
Sanarwar ta ce:
“Cikin cikakkiyar mika wuya ga nufin Allah, Rabaran, limamai, ‘yan’uwa na addini da mabiya Cocin Katolika na Issele-Uku na sanar da rasuwar Rabaran Dr. Stephen Chukwuma, wadda ta faru a ranar 31 ga Disamba, 2025.
“Har zuwa rasuwarsa, shi ne Limamin Cocin St. John the Baptist, Agbor, kuma Regional Vicar na Yankin Agbor.”

Source: Original
Yaushe za a gudanar da jana'izar marigayin?
Cocin ya kuma bayyana shirye-shiryen jana’izarsa, inda ya ce a ranar Talata, 27 ga Janairu, 2026, za a gudanar da taron addu’ar dare a Cocin St. John the Baptist, Agbor, da karfe 5:00 na yamma.
A ranar Laraba, 28 ga Janairu, 2026, za a gudanar da jana’izar taro a Cocin St. Paul’s Cathedral, Issele-Uku, da karfe 10:00 na safe.
Rasuwarsa ta zo wa al’ummar Katolika a Delta da ma Najeriya baki daya a matsayin babban rashi.
An haife shi a ranar 5 ga Yuni, 1962, a Agbor, amma asalinsa daga Akumazi-Umuocha ne a Karamar Hukumar Ika ta Arewa maso Gabas.
Ya fara hidimar addini tun yana karami a matsayin mai hidimar bagade (altar server) a Cocin St. John the Baptist.
Babban malamin ya yi karatunsa na firamare da sakandare a Agbor, kafin ya shiga makarantar horas da limamai (seminary) a shekarar 1982.
Daga bisani ya yi karatun addini a St. Paul’s Missionary Seminary, Iperu-Remo, da kuma Saints Peter and Paul Major Seminary, Bodija, Ibadan, cewar Leadership.
Babban Fasto ya rasu a Najeriya
A wani labarin, Cocin Katolika na Wukari a jihar Taraba ya tabbatar da rasuwar babban malamin addinin Kirista bayan rashin lafiya.
Marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Wukari, inda ya shafe shekaru yana hidimar Allah cikin tawali’u da jajircewa.
Ana shirin gudanar da jana’izarsa a St Mary da ke Wukari, tare da yi masa wake ranar 19 ga Nuwamba da kuma jana’iza ranar 20 ga wata.
Asali: Legit.ng
