Yunkurin Juyin Mulki: Cafke Malamin Musulunci a Kaduna Ya Bar Baya da Kura

Yunkurin Juyin Mulki: Cafke Malamin Musulunci a Kaduna Ya Bar Baya da Kura

  • Cafke malamin addinin Musulunci da aka yi a jihar Kaduna ya fara tayar da hankula da neman bi masa hakkinsa
  • Masu kare haƙƙin ɗan Adam sun nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamin a Zaria, Sheikh Sani Khalifa
  • An ce an kama malamin ne bisa zargin alaƙa da yunƙurin juyin mulki da ake dangantawa da wasu jami’an sojoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zaria, Kaduna - Ci gaba da tsare wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Zaria, Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir ya fara jawo maganganu.

An ce an kama malamin ne bisa zargin alaƙa da wani shirin juyin mulki da ake dangantawa da wasu jami’an sojoji.

An cafke malamin Musulunci a Kaduna
Sheikh Sani Khalifa na Zaria. Hoto: Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir.
Source: Facebook

Yadda aka cafke malamin Musulunci a Kaduna

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama malamin ne sama da makonni uku da suka gabata, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu: An cafke babban malamin Musulunci a Zaria

Hakan na zuwa ne yayin da ake bincike kan zargin wasu jami’an soja na shirin tayar da tarzoma domin rushe gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Majiyoyi sun ce kama Sheikh Sani Khalifa ya biyo bayan wata mu’amalar kuɗi ta kusan Naira miliyan biyu da aka ce an gano ta shiga asusunsa daga hannun ɗaya daga cikin jami’an sojan da ake bincike a kansu.

Sai dai, yayin da hukumomin tsaro suka ƙi yin cikakken bayani kan cafke shehin malamin, na kusa da malamin sun dage cewa kuɗin kyauta ce da aka ba shi domin yin addu’o’i, Premium Times ta tattaro.

Da yake tsokaci kan lamarin, wani mai sharhi kan harkokin jama’a da ke Zaria, Abu Hamdani, ya bayyana cewa ci gaba da tsare farar hula ba tare da gurfanarwa ba abin damuwa ne ƙwarai.

Ya ce:

“Ba za ka iya ci gaba da tsare ɗan ƙasa bisa zato kawai ba. Idan akwai hujja, a kai shi kotu. Idan babu, a sake shi. Wannan ne kundin tsarin mulki ya tanada.”

Kara karanta wannan

Bam a masallaci: Wanda ake zargi ya fadi makudan kudi da aka ba shi a Borno

An caccaki gwamnati bayan cafke Sheikh Sani Khalifa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Martanin masu karehakkin dan Adam

Haka nan, lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Nababa Umar, ya bayyana shiru da hukumomi suka yi a matsayin abin tayar da hankali.

A kafafen sada zumunta, ra’ayoyin jama’a sun kasu kashi biyu, inda wasu suka ce ya dace hukumomin tsaro su yi tsattsauran bincike domin kare dimokuraɗiyya, yayin da wasu ke gargadin cewa ana tauye ‘yancin jama’a.

Wani masani kan harkokin siyasa, Iliyasu Umar, ya ce gaskiya da bayyana bayanai a fili su ne mabuɗin tabbatar da amincewar jama’a.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su tabbatar da kama Sheikh Sani Khalifa a hukumance ba, kuma ba su bayyana wata tuhuma a kansa ba.

Gwamna zai fara ba malaman addini albashi

Kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal ya waiwaiyi 'dan albashin da ake bai wa malaman addinin Musulunci da limaman Juma'a a jihar Zamfara.

Gwamnan ya tabbatar da cewa ya karbi shawarwarin kwamitin da ya kafa domin duba albashin malaman, kuma zai fara aiwatarwa a 2026.

Ya bukaci malamai da sauran shugabannin addini su hada kai da gwamnati, kuma su maida hankali wajen shiryar da al'umma zuwa tafarkin zama lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.