Gwamna Bala Ya Ballo Aiki, Hukumar EFCC Ta Yi Masa Wankin Babban Bargo

Gwamna Bala Ya Ballo Aiki, Hukumar EFCC Ta Yi Masa Wankin Babban Bargo

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya fito ya yi zarge-zarge kan hukumar yaki da cin hanci ta EFCC
  • Hukumar EFCC ta musanta zargin da gwamnan ya yi na siyasa wasu 'yan siyasa na amfani da ita don muzguna masa
  • Ta tunatar da gwamnan laifuffukan da ake tuhumarsa da su kafin ya samu damar darewa kan kujerar gwamnan jihar Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta yi magana kan zargin da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi a kanta.

Gwamna Bala ya yi zargin cewa abokan hamayyarsa na siyasa na amfani da hukumar wajen muzguna ma shi da jami’an gwamnatinsa.

EFCC ta ragargaji Gwamna Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da tambarin hukumar EFCC Hoto: @SenBalaMohammed, @OfficialEFCC
Source: Twitter

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma’a, 2 ga watan Janairun 2026, EFCC ta bayyana zargin a matsayin “kagagge".

Kara karanta wannan

PDP ta kausasa harshe kan ficewar Gwamna Mutfwang zuwa jam'iyyar APC

EFCC ta yi wa Gwamna Bala Mohammed martani

Ta bayyana cewa babu gaskiya a zargin kuma ta jaddada cewa ia hukuma ce mai cin gashin kanta.

Hukumar na mayar da martani ne kan kalaman da aka danganta da Bala Mohammed, inda ya zargi wasu 'yan siyasa, musamman Ministan Abuja, Nyesom Wike, da amfani da EFCC wajen yakar sa.

“EFCC hukuma ce mai zaman kanta da aka kafa domin yaki da laifuffukan tattalin arziki da na kudi."
"Hukumar ba ta bangaranci, tana gudanar da aikinta ba tare da son rai ko kiyayya ba.Don haka kokarin nuna ta a matsayin hukuma mai bin umarnin wasu ‘yan siyasa abin wasa ne kuma abin Allah-wadai.”

- Hukumar EFCC

Gwamna Bala ya fusata hukumar EFCC

EFCC ta ce abin raini ne gwamnan ya danganta ayyukan hukumar a Bauchi da tasirin wani mai rike da mukamin siyasa.

“Abin raini ne Bala Mohammed ya danganta ayyukan hukumar a jihar Bauchi da tasirin Mista Wike. Ya kamata a fayyace cewa babu wani mai mukamin siyasa da ke da ikon tsoma baki ko tasiri kan binciken EFCC.”

Kara karanta wannan

Gwamna Bala da Ministan Abuja sun ja daga, sun fara amfani da kalamai masu zafi

“Idan Bala Mohammed zai yi gaskiya, ya kamata ya sanar da ‘yan Najeriya cewa yana fuskantar shari’ar badakalar kudade a lokacin da ya lashe zaben gwamnan Bauchi."
"Kariyar kundin tsarin mulki daga gurfanarwa da mukaminsa na yanzu ke ba shi ne kawai ya sanya shari’ar ta tsaya cak.To wa ya tilasta wa EFCC ta bincike shi a shekarar 2016 tare da kai shi kotu?”

- Hukumar EFCC

EFCC ta yi wa Gwamna Bala martani mai zafi
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed na jawabi a wajen taro Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Game da shari’o’in da suka shafi wasu jami’an gwamnatin jihar Bauchi, EFCC ta ce duk bayanan sun riga sun shiga gaban kotuna kuma a bude suke ga idon jama’a.

“Kololuwar munafunci ne ‘yan siyasar adawa su rika ihun ana zaluntarsu duk lokacin da aka kira wani nasu ya ba da bayani, amma su yi shiru idan dan jam’iyya mai mulki ya fuskanci irin wannan hali."

- Hukumar EFCC

EFCC na tuhumar kwamishina a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shirya gurfanar da kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a gaban kotu.

Hukumar EFCC ta shirya gurfanar da shi tare da kamfanin Ayab Agro Products and Freight a gaban kotun tarayya Abuja.

Hukumar EFCC na tuhumar kwamishinan da kamfanin ne kan zargin wanke-wanken kudi har Naira biliyan 4.65.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng