Abun Ya Yi Muni: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kebbi, An Rasa Rayuka

Abun Ya Yi Muni: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kebbi, An Rasa Rayuka

  • 'Yan bindiga sun kashe mutane takwas a kauyukan Kaiwa da Gebbe na jihar Kebbi, sannan sun cinna wa gidan shugaban gari wuta
  • Hare-haren sun tilasta wa daruruwan mazauna yankin tserewa zuwa garin Shanga bayan barin saboda tsananin tsoro da fargaba
  • Rundunar yan sandan ta ce jami'an tsaro sun fara gudanar da sintiri na musamman domin kamo 'yan ta'addar da suka aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - An shiga tashin hankali a ƙaramar hukumar Shanga da ke jihar Kebbi, biyo bayan jerin hare-hare da ’yan bindiga suka kai wa wasu ƙauyuka, inda aka tabbatar da mutuwar akalla mutane takwas.

Waɗannan hare-hare, waɗanda aka fara kai wa tun daren Lahadi kuma suka ci gaba har zuwa daren ranar Laraba, sun haifar da gagarumar asarar rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe bayin Allah ana tsaka da murnar shiga 2026 a garin Jos

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kebbi
Jihar Kebbi, inda 'yan bindiga suka kashe mutane akalla takwas. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kebbi

Rahoton TVC News ya nuna cewa daruruwan mazauna yankin sun tsere daga gidajensu domin neman tsira a garin Shanga da sauran yankunan da ake ganin akwai tsaro.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa maharan sun farmaki ƙauyukan Kaiwa, Gelawu, da kuma Gebbe.

A cewarsa, mutane bakwai ne suka rasu nan take yayin harin, yayin da mutum ɗaya kuma ya rasu a asibiti sakamakon raunukan da ya ji.

A ƙauyen Kaiwa, maharan sun aikata danyen aiki inda suka cinna wa gidan shugaban ƙauyen wuta baki ɗaya, baya ga kashe mutane biyar da suka yi a garin.

Haka kuma, an bayar da rahoton kisan wasu mutane a garuruwan Gebbe, Gurwo, da kuma Tungan Giwa a ranaku mabanbanta.

Halin da ake ciki a wasu kauyukan Kebbi

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Nasarawa, an rasa rayukan bayin Allah

Mazauna yankin da suka zanta da manema labarai sun bayyana cewa wannan farmaki ya jefa dukkan yankin cikin fargaba, inda mutane suka baro gonakinsu, dabbobinsu, da sauran kayayyakin amfaninsu saboda tsoron kada a dawo kansu.

Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa:

"Mutane sun rasa komai na rayuwarsu, kuma halin da ake ciki yanzu yana ƙara muni. Iyalai da dama yanzu suna gudun hijira a garin Shanga ba tare da abinci ko matsuguni na gari ba."

Wannan yanayi ya janyo kira na gaggawa daga shugabannin al'umma ga gwamnatin jiha da ta tarayya game da bukatar kai daukin gaggawa a yankin.

'Yan bindiga sun baza jami'ai da 'yan ta'adda suka kashe mutane a Kebbi
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Matakin da 'yan sandan Kebbi suka dauka

Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da cewa an riga an baza jami'an tsaro na haɗin gwiwa waɗanda suka haɗa da sojoji da ƴan sanda domin gudanar da sintiri na musamman a cikin dazuzzukan da ke maƙwabtaka da yankin.

SP Bashir Usman ya jaddada cewa ana ci gaba da gudanar da aikin kakkaba domin kamo ɓata-garin.

Duk da haka, mazauna yankin suna bukatar a samar da sansanin jami'an tsaro na dindindin a yankunan karkara domin ba su damar komawa ci gaba da ayyukansu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ginin kamfani ya rufta kan ma'aikata a Kebbi, mutane sun makale

'Yan bindiga sun kashe mutane a Filato

A wani labari, mun ruwaito cewa, manoma tara ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu mahara sun kai farmaki kauyen Bum da ke Jos ta Kudu a daren ranar Laraba.

Maharan sun kutsa cikin ƙauyen tare da buɗe wuta ba kakkautawa lokacin da mutane ke barci, lamarin da ya jefa yankin cikin firgici da baƙin ciki.

An ce an fara gano gawarwakin mutane shida ne tun da daddare, amma zuwa safiyar ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu, 2026, adadin waɗanda suka mutu ya kai tara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com