Barau Jibrin Ya Kadu Bayan Rasuwar Dan Uwansa Sanata, Ya Tuna Alherinsa
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi jimamin rasuwar Sanata Godiya Akwashiki
- Barau ya bayyana marigayin a matsayin jajirtacce, amintaccen ɗan majalisa da ya yi aiki tuƙuru wajen bunƙasa rayuwar al’ummar
- Sanata Akwashiki, wanda aka fara zaɓen sa a 2019 sannan aka sake zaɓe a 2023, ya rasu yana da shekaru 52
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin ya yi jimamin mutuwar daya daga cikin sanatoci a Najeriya da ya rasu a India.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ce tabbas sun yi rashin amini kuma jajirtacce mutum, Sanata Godiya Akwashiki.

Source: Twitter
Barau ya jajanta kan rasuwar Sanata Godiya
Hakan na cikin wani rubutu da sanatan ya yi a shafinsa na X a yau Alhamis 1 ga watan Janairun 2026 wanda Legit Hausa ta gano.
Barau ya bayyana jimaminsa kan rashin kwararren dan majalisar daga mazabar Nasarawa ta Arewa.
An tabbatar da cewa marigayin ya rasu a ranar Laraba 31 ga watan Disambar 2025 a wani asibiti da ke kasar India.
A cikin rubutunsa, Barau ya ce:
"Ina jimamin rasuwar abokina kuma ƙwararren ɗan majalisar dattawa, Sanata Godiya Akwashiki (Nasarawa ta Arewa), wanda ya rasu a wani asibiti a ƙasar Indiya a ranar Laraba.
"Sanata Akwashiki ya kasance fitaccen ɗan majalisa wanda ya yi aiki tuƙuru domin inganta rayuwar al’ummar mazabar Nasarawa ta Arewa da ma sauran sassan jihar."
Sanata Barau ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da dukkan al'ummar mazabarsa da kuma jihar Nasarawa.
Ya yi addu'ar Allah ya ba su hakurin jure rashin marigayin inda ya ce zai yi wahala a iya maye gurbinsa.
Ya ce:
"Ina jajantawa iyalansa na kusa, da dukkan al’ummar mazabar Nasarawa ta Arewa na Jihar Nasarawa gaba ɗaya.
"Allah ya ba su ƙarfin zuciya da juriya wajen ɗaukar wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba."

Source: Facebook
Barau ya fadi halayen marigayi Sanata Godiya
Sanata Barau ya ce marigayin ya nuna cikakken kishin ƙasa da jajircewa wajen gina Najeriya ta hanyar gudummawar da ya bayar a ciki da wajen Majalisar Dattawa.
An haifi Sanata Akwashiki a Angba Iggah, Karamar Hukumar Nasarawa Eggon ta Jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
An fara zaɓen sa a Majalisar Dattawa a shekarar 2019, sannan aka kuma zaɓen sa a shekarar 2023 kafin sanatan ya rasu a jiya Laraba yana da shekaru 52.
Barau ya jajanta rasuwar 'yan majalisar Kano
A baya, mun ba ku labarin cewa Sanata Barau I. Jibrin ya yi matukar jimami tare da mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu ranar Laraba 23 ga watan Disambar 2025.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce wannan babban rashi ne ga al'ummar mazabun 'yan Majalisar da kuma gwamnatin jihar Kano.
Barau ya yi addu'ar Allah SWT Ya gafarta masu kura-kuransu, Ya bai wa iyalansu hakuri da juriyar wannan babban rashi da al'umma ta yi.
Asali: Legit.ng

