Yan Bindiga Sun Kutsa Fada da Karfi da Dare, Sun Sace Sarki Da ’Dansa

Yan Bindiga Sun Kutsa Fada da Karfi da Dare, Sun Sace Sarki Da ’Dansa

  • Wasu yan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan a fadar wani Sarki da ke wani yanki a jihar Kwara
  • Maharan sun sace Sarkin Aafin, Oba Simeon Olaonipekun, tare da ɗansa Olaolu bayan kai farmaki fadarsa
  • Al’umma sun shiga fargaba yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin ceto sarkin da ɗansa daga hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ile Ere, Kwara - Fargaba ta mamaye al’ummar Aafin da ke yankin Ile Ere, a Karamar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara, bayan sace Sarki.

An tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun sace Sarkin yankin, Oba Simeon Olaonipekun da dare bayan sun farmaki fada.

Yan bindiga sun sace Sarki da dansa a Kwara
Gwamna Abdulrahman Abdulrazak na Kwara da Oba Simeon Olaonipekun. Hoto: Kwara State Government.
Source: Facebook

Yan bindiga sun sace Sarki a Kwara

Rahotanni daga Channels TV sun ce an sace Sarkin ne tare da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa da ake kira Olaolu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa dajin Sambisa, sun yi kaca kaca da Boko Haram

Wannan mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai wa fadarsa ya faru ne a daren Laraba 31 ga watan Disambar 2025.

An bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, inda kimanin ‘yan bindiga takwas suka kutsa cikin fadar, suna harbe-harbe ba tare da tsari ba kafin su tilasta shiga cikin ginin.

Wani ɗan uwa da ke cikin fadar a lokacin harin ya shaida cewa ‘yan bindigar sun zo ne kai tsaye domin sarkin da matarsa.

Ya ce:

“Na lura da wasu da ba a saba gani ba a waje da misalin ƙarfe 8:00 na dare, sai na faɗakar da mutanen da ke ciki. Mun fara kulle ƙofofi tare da kashe fitilu, amma da suka fahimci haka, sai suka fara harbi.”
Yan bindiga sun sace Sarki bayan kutsawa fadarsa a Kwara
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda yan bindiga suka fasa fada

A cewarsa, maharan sun fasa ƙofofin fadar da makamai, tare da neman ganin basaraken, Sarkin ya fito amma sun harbi matarsa, Felicia Olaonipekun da harsashi.

An ƙara da cewa Olaolu, ɗan Sarkin da ke aikin bautar ƙasa (NYSC), shima an kama shi bayan da ya fito daga inda ya buya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe bayin Allah ana tsaka da murnar shiga 2026 a garin Jos

Majiyar ta ce mutane kusan 10 ne ke cikin fadar a lokacin, kasancewar sun zo hutun bikin ƙarshen shekara tare da sarkin.

Bayan tafiyar ‘yan bindigar, aka garzaya da matar Sarkin asibiti a daren ranar domin ba ta kulawar gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan sa-kai masu tsaron al’umma ba su iya dakile harin ba, saboda mutum biyu kacal ne ke bakin aiki.

Majiyar ta ƙara da cewa shugaban ‘yan bindigar yana magana da Ingilishi sosai, kuma sun nufi fadar kai tsaye ba tare da kai hari wani wuri a garin ba.

Basarake ya tsira bayan garkuwa da shi

Kun ji cewa wani Basarake da yan bindiga suka sace a jihar Kwara ya shaki iskan yanci bayan shafe kusan wata daya ba a san halin da yake ciki ba.

Bayagan Ile a Kwara, Ojibara Kamilu Salami, ya samu ‘yanci bayan biyan kudin fansar da ba a fayyace ba saboda dalilai na tsaro a yankin.

Al’ummar garin sun tarbi basaraken da murna, bayan an biya kudin fansa mai yawa har kashi biyu, wanda jama’ar gari kadai suka tara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.