Albishir da Gwamna Radda Ya Yi ga Al’ummar Katsina game da Ta’addanci
- Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya yi magana game da hare-haren ta'addanci a jihar yana sa ran 2026 za ta yi armashi
- Ya danganta ci gaban tsaro da haɗin kai tsakanin gwamnati, jami’an tsaro, sarakuna da al’umma, yana yaba musu kan jajircewarsu
- Gwamnan ya ce ilimi, noma, kiwon lafiya da gine-gine sun samu ci gaba, yana alƙawarin manyan ayyuka da ingantacciyar rayuwa a 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi albishir ga al'ummarsa game da hare-haren ta'addanci.
Radda ya bayyana cewa zaman lafiya na ƙara dawowa sannu a hankali a jihar, musamman a wasu kananan hukumomi da a baya ‘yan bindiga suka addaba.

Source: Facebook
Radda ya yi hasashen ingantacciyar sabuwar shekara
Ya yi wannan jawabi ne a sakon sabuwar shekara da ya aikawa al’ummar jihar yayin da ake shiga shekarar 2026, cewar Tribune.
Gwamnan ya nuna kyakkyawan fata cewa shekarar 2026 za ta kawo ƙarin ingantuwar tsaro da kuma saurin bunƙasar ci gaba a faɗin jihar Katsina.
Ya ce nasarar da ake samu a fannin tsaro sakamakon haɗin kai ne tsakanin gwamnati, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin al’umma da jama’a gaba ɗaya.
Gwamna Radda ya yaba wa jami’an tsaro, ‘yan sa-kai na tsaron al’umma, sarakunan gargajiya da mazauna jihar bisa goyon baya da haɗin kai da suka bayar wajen yaƙar matsalar rashin tsaro.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na nan daram wajen ƙarfafa nasarorin da aka samu domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a jihar.

Source: Facebook
Radda ya fadi ci gaba fannin ilimi
A bangaren ilimi, gwamnan ya jaddada cewa fannin na ci gaba da kasancewa muhimmin ginshiƙi a ƙarƙashin shirinsa na “Building Your Future”, inda ya ce an ba ɗalibai tallafin karatu da guraben ilimi.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gina da gyara ajujuwa da dama tare da raba kayan karatu masu darajar miliyoyin Naira, domin tabbatar da cewa dukkan yara, ba tare da la’akari da halin kuɗinsu ba, sun samu ilimi mai inganci.
Game da gine-gine, Gwamna Radda ya ce an kaddamar da ayyukan sabunta birane a dukkan mazabun sanatoci uku, inda ake gina hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Ya tabbatar wa al’umma cewa za a ƙaddamar da manyan ayyukan tarihi a shekarar 2026, domin sauya fasalin birane da karkara tare da inganta rayuwar jama’a, cewar Premium Times.
Gwamna Radda ya caccaki masu sukar gwamnoni
Kun ji cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna damuwa kan matsin lambar da ake yi wa gwamnoni a Najeriya.
Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa bai kamata ana dorawa gwamnoni laifi ba duk lokacin da aka samu tsadar rayuwa a kasar wanda ke shafar kowa.
Gwamnan ya nuna cewa gwamnoni fa ba su ba ne ke samun kaso mai tsoka na kudaden da ake rabawa duk wata daga asusun tarayya.
Asali: Legit.ng

