Sojoji Sun Kutsa Dajin Sambisa, Sun Yi Kaca Kaca da Boko Haram
- Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun kai farmaki a cikin Dajin Sambisa inda suka yi artabu da ’yan ta’adda tare da cimma nasara a kansu
- A yayin samamen, an hallaka wasu daga cikin ’yan Boko Haram yayin da sauran suka tsere cikin rudani da suka ji wuta daga dakarun Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun kuma kwato bindiga da harsasai, abin da ke nuna ci gaba da matsin lamba kan masu tada ƙayar baya a dajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai ta sake kai wani gagarumin samame a Dajin Sambisa, inda ta hallaka ’yan Boko Haram tare da kwato makamai.
Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da aikin ne a ranar 29, Disamban 2025, bayan hadin gwiwa tsakanin sojoji da wasu rundunonin sa-kai, lamarin da ya taimaka wajen samun nasara cikin gajeren lokaci.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an ce harin ya kara nuna yadda sojoji ke kara matsa lamba kan maboyar ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, wanda ya shahara da kasancewa wajen buyan Boko Haram da ISWAP tsawon lokaci.
Sojoji sun farmaki Boko Haram a Sambisa
Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun Najeriya ne suka jagoranci wannan samame, tare da hadin gwiwar CJTF, rundunonin hadaka da kuma mafarauta.
An ce tawagar ta tashi daga sansanin sojoji zuwa yankunan Tokumbere da Lagara, a kan hanyar zuwa Sabil Huda domin haduwa da dakarun Najeriya.
A cewar bayanan da aka samu, sojojin sun samu nasarar tsabtace yankunan Tokumbere da Lagara kafin su yi artabu da wasu ’yan Boko Haram da ake zargin suna son yin kwanton bauna ne a hanyar.

Source: Facebook
Wani rahoto ya bayyana cewa farmakin da sojojin suka kai ya biyo bayan bayanan sirri da aka tattara kan motsin ’yan ta’addan a yankin.
Sojoji sun yi artabu da Boko Haram
Majiyoyi sun ce da lokacin artabun da suka yi, sojojin sun yi amfani da karfin bindiga, lamarin da ya kai ga hallaka ’yan ta’addan
Rahotanni sun nuna cewa sauran ’yan kungiyar sun tsere cikin rudani, kuma ana zargin da dama daga cikinsu sun samu raunukan harbin bindiga.
Bayan artabun, dakarun sun ci gaba da bincike da sintiri a yankin domin tabbatar da cewa babu sauran barazana. An ce ba a sake samun wata arangama ba, abin da ya nuna cewa ’yan ta’addan sun watse daga yankin.
A yayin binciken bayan artabu, sojoji sun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da kuma jaka da ke dauke da harsasai da dama.
'Yan ta'adda sun kai hari caji ofis a Ondo
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun kai hari ofishin 'yan sanda a wata karamar hukuma a jihar Ondo.
Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana cewa an bi sawun maharan bayan rusa ofishin 'yan sanda da kona shi da suka yi cikin dare.
Kakakin 'yan sandan jihar ya tabbatar da cewa maharan sun kai akalla 30 kuma sun fara kai hari ne bayan karfe 9:00 na dare a yankin.
Asali: Legit.ng

