Bayan Dangote, MRS, yanzu NNPCL Ya Sauke Farashin Litar Fetur a Wasu Gidajen Mai
- Kamfanin NNPCL ya samu ribar Naira biliyan 502 a Nuwamba, 2025 sakamakon bunkasar gas da kuma farfadowar hakar danyen mai
- Kamfanin ya rage farashin litar man fetur zuwa kasa da N800 domin yin gogayya da farashin matatar man Dangote a kasuwa.
- Gwagwarmayar neman kwastomomi ta sa gidajen man NNPCL, Heyden, AP, da MRS sauke farashin fetur a sassan kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya sanar da samun ribar Naira biliyan 502 a watan Nuwamba na shekarar 2025, duk da kalubalen da aka fuskanta na raguwar hakar danyen mai.
Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa NNPCL ya samar da kudaden shiga har Naira tiriliyan 4.36 a cikin watan, sakamakon bunkasar iskar gas da kuma ingantuwar hanyoyin jigilar mai.

Source: Facebook
NNPCL ta rage farashin litar fetur
Wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da hakar danyen mai ya farfado kadan zuwa ganga miliyan 1.36 a kowace rana, in ji rahoton jaridar Punch.
A daidai wannan lokaci, NNPCL ya shiga sahun gasar rage farashin man fetur a kasar nan domin gogayya da matatun mai masu zaman kansu.
Kamfanin ya rage farashin litar man fetur zuwa kasa da Naira 800, inda wasu gidajen man sa a kan hanyar Legas zuwa Ibadan suka fara sayar da lita a kan Naira 785.
Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba daga kasuwa, musamman bayan da matatar man Dangote ta rage farashin lita zuwa Naira 739 a wasu gidajen mai.
Gasar kasuwa Ta tilasta rage farashin mai
Bincike ya nuna cewa NNPCL ya fuskanci karancin kwastomomi a makonni biyun da suka gabata lokacin da yake sayar da lita a kan Naira 875, yayin da wasu gidajen mai ke sayarwa a kan Naira 739.
Wannan gasar ta sa jami'an NNPCL rage farashin akai-akai daga N845 zuwa N825, har ya zuwa matakin yanzu na kasa da N800.
Masana sun nuna cewa ko da yake farashin shigo da man daga kasashen waje ya kai kusan N828, dole ta sa NNPCL sayarwa a kasa da haka domin kada ya rasa kwastomominsa ga matatar Dangote.

Source: Facebook
Gasar sayar da fetur a gidajen man Najeriya
Cikakken sassauta ikon gwamnati kan farashin mai ya sanya gasa ta zama ruwan dare a tsakanin masu gidajen mai irin su Heyden, AP, da MRS.
Wannan yanayi ya kawo karshen dogayen layuka da aka saba gani a gidajen man NNPCL a baya.
A halin yanzu, NNPCL tana kokarin daidaita tsakanin samun riba a ayyukanta na iskar gas da kuma rike matsayinta a kasuwar sayar da man fetur ta hanyar rage farashi domin amfanin talakan Najeriya.
Legit ta ziyarci MRS Kaduna
Wakilin Legit Hausa da ya ziyarci gidan man MRS da ke Constitution Rd, Kakuri, Tudun Wada, Kaduna, ya tarar da masu ababen hawa na layin sayen fetur a farashi mai sauki.

Kara karanta wannan
Duk da karancin danyen mai, NNPCL ya samu ribar fiye da Naira biliyan 502 a wata 1
Wakilin ya ce gidan man yana sayar da litarsa a kan N739, wanda ya yi dai dai da sanarwar da matatar Dangote ta fitar, na cewa haka MRS zai rika sayar da feturinsa.
Wani mai mota, Kayode Chukudi, ya bayyana cewa:
"Wannan ragi ne ya sa ina shigowa Kaduna daga Abuja na wuto ta nan, ina so na cika tanki na kafin na shiga gari, har in gama abin da zan yi ban sayi wani mai ba.
"Mu muna jin dadin wannan sauyi da aka samu, muna so a ci gaba da samun saukin fetur, ai talaka ya dade yana shan wahala, musamman lokacin da aka yi wahalar man."
Wani mai tuka adai daita sahu, Man Nas, ya ce:
"Ka ga keke na CNG ce, amma wani lokaci na fi gane wa zuwa nan gidan man in sanya fetur, saboda mansu yana rike wuta, ba ya saurin konewa, ga kuma arha.
"Sai idan man ya kare ne nake komawa CNG, mu kasar nan kawai dole mutum ya koyi maneji, akwai wurin da zan mayar cng, akwai wurin da fetur zan mayar."
An sauke farashin fetur a jihohin Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta fara sayar da litar fetur a kan farashin ₦739 a dukkan gidajen mai na MRS a faɗin Najeriya.
An sauke farashin ne domin rage wahala ga ’yan Najeriya musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Matatar Dangote ta gargadi masu ƙoƙarin ƙirƙirar ƙarancin man fetur tare da kira ga hukumomi su ɗauki tsauraran matakai a kai.
Asali: Legit.ng


