'Tinubu Ya Cikawa Kabilar Ibo Burinsu na Son Kafa Kasar Biyafara,' Umahi

'Tinubu Ya Cikawa Kabilar Ibo Burinsu na Son Kafa Kasar Biyafara,' Umahi

  • Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika burin da al’ummar Igbo suka dade suna nema wajen fafutukar Biyafara
  • Umahi ya bayyana shekarar 2026 a matsayin “shekarar cigaba” ga yankin Kudu-maso-Gabas, yana mai yabawa manufofin tattalin arzikin Tinubu
  • A bayanin da ya yi, Umahi ya bukaci Igbo su haɗa kai su mara wa Tinubu baya a zaben 2027, yana gargadin kada su sake kuskure irin na zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ministan Ayyuka, David Umahi, ya sake nanata cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa al’ummar Igbo abin da ya bayyana a matsayin “Biyafara” da suka dade suna nema, ta hanyar cikakken shigar da su cikin harkokin mulkin ƙasa.

Umahi ya bayyana hakan ne a sakon sabuwar shekara da ya fitar, inda ya yaba da manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya tare da hasashen samun gagarumin sauyi a fannoni daban-daban a nan gaba.

Kara karanta wannan

Babban Sarki ya bar duniya kwana 1 kafin bikin zagayowar ranar haihuwarsa

Ministan ayyuka tare da shugaban kasa
David Umahi da shugaban kasa Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa ministan ya ce shekarar 2026 za ta kasance “shekarar cigaba” ga yankin Kudu-maso-Gabas, bayan shekaru na abin da ya kira wulakanci da wariya daga gwamnatocin baya.

Tinubu ya ba Ibo Biyafara inji Umahi

Ministan ya bukaci al’ummar Igbo da su rungumi abin da ya kira sake fasalin tunani da kawar da tsattsauran ra’ayi, domin su fahimci cewa Biyafara da suka dade suna nema ta zo ne ta hanyar haɗin kan ƙasa, ba rarrabuwa ba.

A cewarsa, Tinubu ya samar da wannan buri ta hanyar aiki da Igbo a matsayin cikakkun ‘yan ƙasa masu cin gajiyar ci gaban ƙasa a Najeriya

A ranar 14, Disamban 2025 ma, Umahi ya yi kira ga Igbo a sassan duniya da su daina neman kafa Biyafara, yana mai cewa gwamnatin Tinubu ta magance korafe-korafen tarihi ta hanyar haɗin kai da daidaito a mulkin ƙasa.

Umahi ya yi wa Tinubu kamfen

Kara karanta wannan

Zulum ya nemi gafarar 'yan Borno, ya ja kunnen masu neman kujerarsa

Ministan ya bukaci al’ummar Igbo da su tsaya tsayin daka wajen marawa Shugaba Tinubu baya, musamman dangane da burinsa na sake tsayawa takara a zaben 2027.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na sanya hannu kan wata takarda. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Umahi ya bayyana cewa ya yi imani yankin zai gyara abin da ya kira kuskuren zaben 2023, inda ya ce Igbo za su tashi tsaye su kada ƙuri’a cikin haɗin kai domin Tinubu.

Ya ce:

“Na yi imani cewa al’ummar Kudu-maso-Gabas za su goge kuskuren zaben 2023, su kuma yi magana da murya ɗaya ta hanyar kada ƙuri’a mai yawa ga Shugaba Tinubu, wanda ya warware matsalar wariya da yankin ya dade yana fuskanta.”

Umahi ya ƙara da cewa al’ummar Igbo ba za su sake yarda da ‘yan siyasa masu yaudara da kalamai masu daɗi ba, yana mai gargadin cewa lokaci ya yi da za su fahimci inda muradunsu suke.

Yahaya Bello zai yi takara a 2027

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya bayyana aniyar tsayawa takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a 2027.

Yahaya Bello ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi tare da sakarakunan gargajiya da shugabannin addini a wata masarauta da ya ziyarta.

A yanzu haka dai Sanata Natasha Akpoti daga jam'iyyar PDP ce ke rike da kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya, inda ake hasashen za su fafata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng