Dalibai Za Su Mamaye Aso Rock, An Sanya Ranar Zanga Zangar Adawa da Harajin Tinubu

Dalibai Za Su Mamaye Aso Rock, An Sanya Ranar Zanga Zangar Adawa da Harajin Tinubu

  • Kungiyar daliban Najeriya ta ayyana ranar 14 ga Janairu a matsayin ranar zanga-zangar adawa da dokokokin harajin gwamnatin Bola Tinubu
  • Shugaban NANS ya soki shugaban hukumar FIRS kan gazawa wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin fara aiwatar da dokar haraji
  • Daliban sun bayyana cewa tilasta wa talakawa sabon haraji a daidai wannan lokaci zai kara jefa al'umma cikin tsananin yunwa da talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ƙungiyar ɗaliban Najeriya ta ƙasa (NANS) ta fara tattara ɗalibai a faɗin ƙasar nan domin gudanar da gagarumar zanga-zanga kan shirin fara aiwatar da sababbin dokokin haraji.

Shugaban ƙungiyar, Kwamared Olushola Oladoja, ya bayyana cewa ɗalibai ba su amince da matakin hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) na fara aiki da wannan doka daga ranar 1 ga Janairu, 2026 ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damƙe ƴan ƙunar baƙin wake 2 kan tashin bam a masallacin Maiduguri

Dalibai za su gudanar da zanga zanga domin nuna adawa da sababbin dokokin haraji.
Dalibai karkashin kungiyar NANS na gudanar da zanga zanga a Abuja. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dalibai sun nuna adawa da dokar haraji

A cewar kungiyar daliban, akwai matsaloli da dama da ba a warware ba a cikin kundin dokar harajin da gwamnatin tarayya ta wallafa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Oladoja ya soki shugaban hukumar FIRS, Dr. Zacch Adedeji, saboda a cewarsa, ya gaza wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin fara aiwatar da sabon harajin.

NANS ta bayyana cewa yunƙurin tilasta wa ‘yan Najeriya wannan doka ba tare da amincewar mafi yawancin jama’a ba ya saɓa wa tsarin dimuƙuradiyya.

Ƙungiyar ta jaddada cewa koda doka tana da kyakkyawar manufa, bai kamata a aiwatar da ita ba muddin majalisar ƙasa da sauran ƙungiyoyin jama'a suna da fargaba akanta.

Dalibai sun sanya ranar zanga zanga

Shugaban na NANS ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnati ta yanke shawarar ci gaba da wannan tsari duk da mawuyacin halin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

'Makaman da Amurka ta harbo Najeriya sun kara tona asirin Gwamnatin Bola Tinubu'

Ya ce ya zama abin kunya yadda aka yi watsi da kukan ƙungiyoyin matasa, ɗalibai, da na farar hula waɗanda suka yi kira da a dakata da dokar har sai an fayyace wasu sassa da ke da sarƙaƙiya, musamman waɗanda suka shafi gaskiya da adalci ga talaka.

Sakamakon haka, NANS ta ayyana ranar Talata, 14 ga Janairu, 2026, a matsayin ranar gudanar da zanga-zangar lumana ta ƙasa baki ɗaya, cewar jaridar Leadership.

Dalibai sun ce za su mamaye fadar Aso Rock a zanga zangar adawa da sababbin dokokin haraji.
Wani bangare na ginin fadar shugaban kasar Najeriya da ke Abuja. Hoto: @NGRPresident
Source: UGC

Dalibai za su mamaye fadar shugaban kasa

Oladoja ya umarci dukkan rassan ƙungiyar na jami'o'i, shiyyoyi, da na jihohi da su fito da ɗalibai masu yawa domin tattaki zuwa ƙofar fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya jaddada cewa mulki na jama'a ne, kuma ikon jama'a ya fi ƙarfin waɗanda ke kan madafun iko, don haka ba za su zuba ido ana cutar da al'umma ba.

Haraji: Tinubu ya samu goyon bayan kotu

A wani labari, mun ruwaito cewa, babbar kotun Abuja ta yi hukunci kan karar da ke neman hana gwamnatin tarayya fara aiwatar da sababbin dokokin haraji.

Kotun ta ba gwamnatin tarayya, hukumar tattara haraji ta FIRS da kuma majalisar tarayya damar ci gaba da aiwatar da sabon tsarin haraji daga 1 ga Janairu, 2026.

Hukuncin da kotun ta yanke ya yi watsi da bukatar da kungiyar Incorporated Trustees of African Initiative for Abuse Public Trustees suka shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com