Dokar Haraji: Gaskiyar Zance kan Batun Cire Kudi daga Asusun Banki
- Wasu 'yan Najeriya na fargabar cewa za a rika cirar kudi a asusun ajiya na bankinsu domin biyan gwamnati kudin haraji
- Shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya fito ya yi bayani filla-filla kan wannan fargabar da ake da ita
- Mista Taiwo Oyedele ya bayyana cewa masu kudi na amfani da talakawa domin yin yaki da sababbin dokokin harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kudi da gyaran haraji, ya yi karin haske kan sababbin dokokin haraji.
Taiwo Oyedele ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sababbin dokokin ba za su janyo cire kudi kai tsaye daga asusun banki ba, komai girman kudin da aka tura ko bayanin da aka yi a kansu.

Source: Facebook
Taiwo Oyedele ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels tv a ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025.
Shin za a rika cire haraji daga banki?
Ya ce babu wata hukuma ta haraji a ko’ina cikin duniya da ke da ikon bibiyar kowane mutum daya bayan daya.
Taiwo Oyedele ya jaddada cewa aiwatar da haraji yawanci na shafar masu samun kudaden shiga masu yawa, ba kananan masu amfani da asusun banki ba.
"Babu wanda zai cire kudi daga asusunka. Duk adadin kudin da ka tura, ko biliyan 1 ne, ko N1, 000 ne, duk irin yadda ka bayyana su. Babu wanda zai cire kudi daga asusun bankinka.”
- Taiwo Oyedele
Ana yada karya kan dokokin haraji
Shugaban kwamitin ya ce damuwar da ake nunawa kan cire kudi daga banki ta samo asali ne daga bayanan karya da ake yadawa.
Ya yi nuni da cewa da yawa daga cikin wadanda ke adawa da gyaran harajin ba sa cikin rukunin masu samun kudin shiga da gyare-gyaren za su shafa.
"Mutanen da suka fi yaki da mu su ne mutanen da ba su da ko Naira miliyan 1 a asusun bankinsu.”
"Kun san hukumar NDIC ta ce kaso 98 cikin 100 na masu asusun banki a Najeriya ba za su iya bugun kirjin suna da N500, 000 a asusunsu ba. Wadannan su ne mutanen da ke fada da mu.”
"Mun ce tsarin da ake da shi yanzu na cutar da talakawa fiye da kima. Bari mu mai da shi na adalci."
"A gaskiya, a daya daga cikin tarurrukanmu, mun ce zai yi wuya masu kudi su fito su yi zanga-zanga, domin ba sa son mutane su san cewa su masu kudi ne.”
“Mun raina yadda wadannan mutane za su iya yaudarar talaka ya yi musu yaki. Ko da kuwa hakan na cutar da muradun talakan kansa, haka abin ya faru, kuma abin mamaki ne matuka."
- Taiwo Oyedele

Source: Facebook
Mutane za su rika ba da bayanai
Ya bayyana cewa sababbin dokokin harajin sun dogara ne kan bayyana kudin shiga kai tsaye, inda ake sa ran masu biyan haraji za su bayyana kudin shigarsu a karshen shekara sannan su biya haraji yadda ya dace.
A cewarsa, mutanen da aka ware daga biyan haraji za su bayyana abin da suke da shi, yana mai jaddada cewa ana saukaka tsarin domin karfafa mutane su bi doka cikin aminci.

Kara karanta wannan
Kamfanin JED ya nemi masallatai da coci su rika biyan kudin lantarki a jihar Gombe
Masanin tattalin arzikin ya zargi manya da yaudarar marasa hali wajen yakar abin da zai cutar da talaka ba.
Tinubu ya dage kan dokokin haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana lokacin fara aiwatar da sababbin dokokin haraji.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa za a fara aiwatar da sababbin dokokin a cikin watan Janairun shekarar 2026 da za a shiga.
Ya bayyana cewa ya lura da korafe-korafen da ake yi, amma bai ga wata babbar matsala da za ta sanya a fasa aiwatar da sababbin dokokin ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

