Tashin Hankali: Ginin Kamfani Ya Rufta kan Ma'aikata a Kebbi, Mutane Sun Makale

Tashin Hankali: Ginin Kamfani Ya Rufta kan Ma'aikata a Kebbi, Mutane Sun Makale

  • Ma'aikaci daya ya rasu yayin da wasu biyar suka makale bayan rushewar wani bangare na kamfanin shinkafa a birnin Kebbi
  • Mataimakin gwamna, Umar Abubakar Tafida ya ziyarci wurin kuma ya ce jami'an agaji na kokarin ceto wadanda ginin ya danne
  • Gwamnatin jihar Kebbi ta lashi takobin kaddamar da bincike mai zurfi domin gano musabbabin rugujewar ginin a yammacin Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - An tabbatar da mutuwar ma'aikaci ɗaya yayin da wasu biyar suka maƙale bayan wani ɓangare na wani babban kamfanin sarrafa shinkafa ya rufta kansu a Kebbi.

Wani mummunan hatsari, wanda ya faru a yammacin ranar Talata, 30 ga Disamba, 2025, ya girgiza al'ummar Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Ginin kamfanin shinkafa ya rufta kan ma'aikata, mutum 1 ya mutu
Taswirar jihar Kebbi, inda ginin kamfanin shinkafa ya rufta kan ma'aikata. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ginin kamfani ya rufta kan ma'aikata a Kebbi

Jaridar Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a kamfanin NIA-AGRI, wanda yake ɗaya daga cikin manyan masana'antun da ke samar da ayyukan yi a yankin.

Kara karanta wannan

'An fara ruwan kudi': Gwamna ya biya ma'aikata albashin watan 13 bayan Kirsimeti

Har zuwa daren ranar, jami'an agajin gaggawa na fafutukar ganin sun ceto waɗanda baraguzan ƙarfe da sauran kayyayakin aiki suka danne.

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya jagoranci wata tawagar gwamnati mai ƙarfi zuwa wurin da abin ya faru domin gudanar da binciken gani da ido.

Tafida ya bayyana damuwarsa ƙwarai, inda ya tabbatar wa iyalai da ma'aikatan kamfanin cewa gwamnati za ta tura dukkan kayan aikin da ake buƙata domin ganin an ceto waɗanda ke raye.

A cewar mataimakin gwamnan:

"Amincin ma'aikata shi ne babban abin da gwamnati ta sa a gaba, kuma ba za mu huta ba har sai mun tabbatar da halin da kowane ma'aikaci yake ciki."

Ana kan gudanar da aikin ceto mutane

Injiniyan da ke kula da ayyuka a wurin ya shaida wa tawagar gwamnati cewa mutum ɗaya ya riga ya riga mu gidan gaskiya nan take bayan rushewar ginin, in ji rahoton Channels TV.

A halin yanzu, rundunar jami'an kashe gobara ta jihar Kebbi da sauran hukumomin agaji suna amfani da manyan injinan haƙo ƙasa da masu yanke ƙarfe wajen gudanar da aikin ceto.

Kara karanta wannan

'Ba mu so': 'Yan majalisa sun fusata da gwamnati ta tura masu kyautar N100,000

Jami'ai sun bayyana cewa aikin yana da matuƙar wahala saboda yanayin yadda ginin ya rushe, don haka dole ne su yi aikin cikin taka-tsantsan domin kada ragowar ginin su faɗo wa ma'aikatan ceto ko su ƙara raunata waɗanda ke ƙasa.

Gwamnatin Kebbi ta lashi takobin gudanar da bincike kan rushewar ginin kamfanin shinkafa.
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya na dagawa al'umma hannu a wani taro a Birnin Kebbi. Hoto: @NasiridrisKG
Source: Twitter

Gwamnati za ta yi bincike kan ruftawar ginin

Wannan hatsarin ya janyo ce-ce-ku-ce game da yanayin tsaro da kariya a masana'antu masu zaman kansu, musamman a jihar Kebbi da take fafutukar zama cibiyar sarrafa shinkafa a Najeriya.

Mataimakin gwamnan jihar ya lashi takobin cewa gwamnati za ta kaddamar da bincike na musamman bayan kammala aikin ceto domin gano ko an bi ƙa'idojin gine-gine da tsaron ma'aikata.

Sanata Umar Tafida ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan ma'aikacin da ya rasu, tare da addu'ar Allah ya tseratar da waɗanda suka maƙale.

Abin fashewa ya tashi a asibitin Kebbi

A wani labari, mun ruwaito cewa, hankulan mutane sun tashi bayan wani abin fashewa ya tashi da sassafe a wani asibitin gwamnati da ke jihar Kebbi.

Lamarin wanda ya jefa mutane cikin firgici da tashin hankali ya auku ne da safiyar ranar Talata, 30 ga watan Disamban 2025.

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana matakan da ta dauka domin shawo kan matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com