Matasa Sun Fito daga Gidan Gwamnati, Sun Yi Wa Mata Masu Zanga Zanga Dukan Tsiya
- Wasu mata da suka gudanar da zanga-zanga a bakin gidan gwamnatin Kwara sun kwashi kashinsu a hannu
- Matan daga Oke-Ode a karamar hukumar Ifelodun sun yi zanga-zangar lumana kan matsalar tsaro da sace-sacen mutane
- Shaidu sun ce wasu mutane dauke da sanduna sun fito daga Gidan Gwamnati suna dukan matan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara – Zanga-zangar lumana da mata suka gudanar a karshen mako kan matsalar tsaro ya rikide zuwa tashin hankali.
Matan na neman daukin gaggawa kan matsalar tsaro a Oke-Ode, karamar hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara.

Source: Twitter
Matasa sun ci 'zarafin' mata masu zanga-zanga
Daily Trust ta ruwaito cewa matan sun taru ne domin jan hankalin gwamnati kan hare-haren ‘yan ta’adda.
Sun koka kan ci gaba da tsare mazajensu da ‘ya’yansu da masu garkuwa da mutane ke yi na tsawon lokaci.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa wadanda aka sace, ciki har da mazajensu, sun shafe watanni a hannun masu garkuwa da mutane ba tare da ganin wani gagarumin mataki daga gwamnati ba.
A yayin zanga-zangar, shaidu sun ce wani rukuni na maza dauke da sanduna sun fito daga cikin Gidan Gwamnati, inda suka fara dukan mata, lamarin da ya tilasta musu tserewa domin tsira da rayukansu.
Bidiyoyin ya bazu a kafafen sada zumunta wanda ya nuna yadda ake bulala da fatattakar matan, yayin da suke ihu suna neman taimako.
Wasu shaidu sun kuma zargi ‘yan sanda da ke wurin da kasa shiga tsakani domin dakile harin.
A cikin wani bidiyo, an ji wata mata tana cewa:
“Don Allah a taimake mu, muna cikin halin wahala game da ayyukan masu garkuwa da mutane a Oke-Ode.”
Harin ya haifar da martani da Allah-wadai daga mazauna jihar da kungiyoyin fararen hula.
A ranar Litinin 29 ga watan Disambar 2025, shugabannin adawa yayin wani hira da yan jaridu sun yi tir da lamarin.
Sun bayyana abin da ya faru a matsayin “cin zarafin tsofaffin mata” da suka fito zanga-zangar lumana domin jan hankalin gwamnati kan matsalar tsaro a yankunansu.
Sun kuma yi zargin cewa ‘yan daba na jam’iyyar APC ne aka sako wa matan domin cin zarafinsu.

Source: Original
Martanin gwamnan Kwara kan dukan masu zanga-zanga
Sai dai a martaninsa ta shafin gwamnatin jihar na Facebook, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya musanta duk wani hannu da gwamnatinsa ke da shi a harin.
Gwamnan ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, yana mai cewa lamarin ya sabawa ka’idoji da manufofin gwamnatinsa.
Gwamnan Kwara ya gargadi yan ta'adda
Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya halarci bikin yaye sababbin jami'an tsaron dazuka da aka horas.
Abdulrahman Abdulrazaq ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen kawo shirin samar da jami'an domin tunkarar matsalar rashin tsaro.
Hakazalika, ya aika da sakon gargadi ga 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane wadanda ke addabar jihar Kwara.
Asali: Legit.ng

